Ɗan bindigar da ake tuhuma da ta'asar kisan jama'a a Norway ya amsa kai harin.
July 24, 2011Yayin da al'umar ƙasar Norway ke cigaba da jimamin mutane 92 ɗin da suka rasu a harin bam da kuma harbin bindiga, mutumin da ake zargi da aikata hare haren biyu ya amsa cewa shi ya aikata ta'asar. Lauyan dake kare matashin mai shekaru 32 da haihuwa ya shaidawa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa wanda yake karewa ya ɗauki lokací mai tsawon yana shirya aiwatar da harin. Waɗanda suka ganewa idanunsu sun ce ɗan bindigar ya yi shigar kayan 'yan sanda ne ya kuma buɗe wuta kan mai uwa da wabi akan taron matasa a wurin shaƙatawa dake tsibirin Utoeya a arewa maso gabashin birnin Oslo. Yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su matasa ne. 'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike domin gano ko akwai wani da suka aikata harin tare da ɗan bindigar. Firaministan Norway Jens Stoltenberg ya baiyana harin da cewa shine abu mafi muni da ƙasar ta gani tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu