2019: Rajin kare muhalli ya ja hankali
Matsalar gurbacewar muhalli na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a shekarar 2019 da muka yi bankwana da ita domin mutane da dama sun yi zanga-zanga ta ganin an alkinta muhalli a fadin duniya.
Janairu: Jamus ta sa ranar rufe wajen hakar kwal
Bayan da aka jima ana tattaunawa, gwamnati ta sa ranar daina amfani da kwal don samar da makamashi a shekarar 2038. Masu rajin kare muhalli sun ce an sanya wa'adin a lokacin da aka rigaya aka makara. Yanzu haka kashi 40 cikin 100 na makamashin da Jamus ke samarwa daga kwal yake kuma ta gaza cimma wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma a 2015 a Paris kan kare muhalli.
Febrairu: Narkewar kankara
Wani bincike da masana kimiyya suka yi na tsawon shekaru biyar ya nuna cewar kashi biyu bisa uku na kankarar da ake da ita a yankin nan na Hindu-Kush-Himalaya za ta narke nan da shekarar 2100 muddin ba a rage fidda hayaki da ke gurbata muhalli ba.
Maris: Mahaukaciyar guguwar Idai ta yi ta'adi a Afirka
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wannan ibtila'i a matsayin mafi muni da aka samu a Muzambik da Zimbabuwe da kuma Malawi, inda mutane kusan dubu suka rasu. Gonaki da dama sun lalace sannan an samu yaduwar cutuka da karancin abinci. Makwanni shidda bayan faruwar lamarin, wata mahaukaciyar guguwar ta sake afka wa yankin.
Afrilu: Zanga-zanga ta haifar da tsaiko
Kungiyar masu rajin kare muhalli ta Extinction Rebellion ta haifar da tsaiko na sufuri na kusan mako guda a birnin London na Birtaniya. 'Yan kungiyar sun yi ta zanga-zanga da nufin ganin sun yi matsin lamba ga hukumomi na dakatar da gurbata muhalli sai dai wasu na ganin kamar da wuya mafarkinsu na son ganin an daina amfani da mai a motoci ya tabbata.
Mayu: Rajin kare muhalli ya karade nahiyar Turai
A zaben majalisar dokokin EU na wannan karon an samu fitar masu kada kuri'a sosai inda masu fafutukar kare muhalli suka samu tagomashi a zaben. Jam'iyyun da ke rajin kare muhalli sun samu kujeru 74 daga cikin 751. Jam'iyyar Greens ta Jamus ta samu kashi 20 cikin 100 na wannan adadi wanda shi ne mafi girma da aka gani. EU ta ce za ta rage fidda hayaki mai guba da kashi 55 ciki 100 nan da 2030.
Juni: Zanga-zangar kare muhalli ta koma kan kwal
Dubban masu rajin kare muhalli sun shiga wajen tonon kwal na Garzweiler da ke birnin Kolon na Jamus, inda suka yi zanga-zanga kan shirin fadada wajen da ake, daidai lokacin da mutane kimanin dubu 40 suka yi zanga-zanga a Aachen ta ganin an alkinta muhalli kuma a wannan lokacin ne majalisar dokokin Birtaniya ta zama ta farko da ta ayyana kare muhalli a matsayin abu mai muhimmanci.
Juli: Yanayin zafi ya karu
Galibin kasashen Turai sun samu karuwar zafi inda ya kai maki 40 a ma'unin Celcius a wasu yankunan. Wannan abu ne da aka jima ba a saba ganin irinsa ba. A lokacin an baiwa mutane shawara kan su kasance a cikin gida sannan su guji yin tafiye-tafiye yayin da aka rika samun jinkiri a fannonin sufuri ciki har da na jiragen kasa.
Augusta: Gobara a dajin Amazon
Yawan gobarar da aka samu a dajin Amazon ya karu har ma ya zarta na shekarar 2010. Ma'aikatan kashe gobara da dama sun yi ta kokari wajen shawo kan wutar daidai lokacin da shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya caccaki kasashen duniya kan abinda suka kira rashin yin wani abun a zo a gani wajen shawo kan wutar.
September: Greta Thunberg
Matashiyar nan 'yar rajin kare muhalli Greta Thunberg wadda ta bijiro da zanga-zangar nan ta Fridays for Future ta soki shugabannin duniya wajen gaza daukar kwakkwaran mataki kan kare muhalli. A wani jawabinta a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Thunberg ta ta ce sauyi na tafe ko an so ko an ki. Kasashen duniya da dama sun yi alkawarin daukar mataki nan da 2050 amma banda wasu manyan kasashe.
Oktoba: Shigar da kara kan kare muhalli
'Yan fafutuka a fadin duniya sun yi ta kai kara kotu kan lamuran da suka danganci kare muhalli a shekarar 2019. A watan Oktoban shekarar kadai wasu kungiyoyin matasa sun yi karar gwamnatin Kanada kan keta yarjejeniyar kare muhallli. A Jamus ma an shigar da kara irin wannan sai dai kotu a Berlin ta yi watsi da karar wadda wasu manoma suka yi.
Nuwamba: Karuwar ambaliya
Birnin Venice na Italiya ya yi fama da ambaliyar ruwa don an samu hakan kusan sau uku a mako guda inda ruwan ya shanye wurare da yawa. Rabon da a ga haka tun cikin shekarar 1872. Gidajen adana kayan tarihi da fitattun wurare na daga cikin inda wannan ambaliya ta shafa. Masu yawon bude idanu sun yi ta daukar hotunan ambaliyar kamar yadda ake iya gani a nan sama.
Disamba: 'Dole a dakatar da gurbata muhalli'
A lokacin da shugabannin duniya suka hadu a birnin Madrid wajen taron sauyin yanayi na COP25, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce duniya ta doshi abin da ya kira "inda ba za a iya dawowa ba". Wani rahoton Kungiyar EU ya ce yanayin da muhalli ke ciki ya munana kuma Turai na iya gaza kaiwa ga kudurin da ta sa a gaba na rage hayaki mai guba nan da shekarar 2030.