Burundi ta rufe ofishin kare hakkin dan Adam
December 6, 2018Talla
Gwamnatin Burundi ta bukaci hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta rufe ofishinta da ke kasar, a watannin baya hukumar ta soki mahukunta bisa take hakkin dan Adam da ake samu a kasar ta Burundi.
Mai magana da yawun hukumar ta ce a wannan Alhamis suka samu takarda daga mahukuntan Burundi kan a rufe ofishin na hukumar kare hakkin dan Adam. A farkon wannan shekara ta 2018 shugabana hukumar mai barin gado Zeid Ra'ad al-Hussein ya baiyana Burundi a matsayin kasar da ta yi kaurin suna wajen zubar da jinin dan Adam, bisa matakan cin zarafin al'uma da gwamnatin Shugaba Pierre Nkurunziza ta Burundi ke dauka sakamakon rikicin siyasa da kasar ta samun kanta a ciki.