A cikin hotuna: Matsanancin yanayi na damina ya girgiza duniya
Daga Jamus zuwa Kanada da Chaina, hotunan ambaliyar ruwa sun mamaye kafofin yada labarai cikin 'yan makonnin nan. Ana iya danganta matsalar da yanayi?
Ambaliyar ruwa a kasashen Turai
Ambaliyar da ba a taba ganin irinta ba daga ruwan saman yini biyu kwatankwacin na watanni biyu, ya jagoranci mummunar asara a yammacin Turai, akalla mutane 209 suka mutu a Jamus da Beljiyam. Tsawon awoyi aka dauka koguna da koramu na cika suna batsewa, ambaliyar ta kuma share wasu tsofaffin yankuna masu tarihi. Sake gina wuraren da suka lalace dai zai ci biliyoyin Euro.
Yanayin damina mai tsanani
Yanayin damina mai tsanani ya kuma ritsa da wasu yankunan Indiya da Chaina, koguna da magudanun ruwan sun yi ambaliyar da ta lalata tashar jirgin kasa ta birnin Zhengzhou da ke tsakiyar Chaina. Gomman mutane sun mutu. Masana kimiyya sun yi hasashen karuwar ruwan sama mai karfi saboda sauyin yanayi. Iska mai dumi za ta janyo karin ruwan sama.
Matsanancin zafi a Amirka da Kanada
Ana kara sabawa da yanayi mai zafi kamar yadda ya kasance a karshen watan Yuni a jihohinn Washington da Oregon na Amirka da gundumar Columbia na Kanada. Yanayi na matsanancin zafi a yankunan, ya janyo mutuwar daruruwan mutane da ake dangantawa da shi. A kauyen Lytton yanayin zafi ya kai digiri 49.6 a ma'aunin Celsius.
Wutar daji da ke haifar da hadari
Duk da cewar yanayin zafi ya shige, sai dai bushewar wurare na tsananta wutar jeji da ba a taba ganin irinda ba. Wutar jejin da ke ci a Oregon, wan da ya koke babban wuri da ya kai girman Los Angeles cikin makonni biyu, ya yi girman da hayakinsa ya isa birnin New York.Bincin da ak gudanar ya danganta matsalar yanayi da halayyar dan Adam.
Gandun jejin Amazon ya kusan karewa ne?
Daga kudu zuwa tsakiya, Brazil na fuskantar mafi munin fari cikin shekaru 100, akwai karuwar hadarin wutar jeji da sare bishiyoyi a gandun dajin Amazon. Masu bincike sun ruwaito cewar yankin Kudu maso Gabashin jejin Amazon ya daina shan ruwa sai dai fitar da hayaki mai dumama yanayi na Carbon Dioxide (CO2), batu da ke ingiza gandun jejin zuwa kololuwarta.
'Gab da yunwa'
Bayan shekaru na fari mai ɗorewa, sama da mutane miliyan 1.14 a Madagascar ba su da wadatar abinci, wanda ya tilasta wasu cin ɗanyen itatuwa, ganyen daji da fara a cikin yanayi mai kama da yunwa. Duk da rashin bala'i daga Indallahi, ko rikicin siyasa, ana danganta halin da kasar ta yankin Kudu maso Gabashin Afirka ke ciki a matsayin "Fari na zamani" mai asali da sauyin yanayi.
Mutane na tserewa bala'o'i
Yawan mutanen da ke tserewa rigingimu sun karu fiye da na shekaru 10 a 2020, inda mutane miliyan 55 suka sauya matsugunai a cikin kasashensu. Daura da wasu miliyan 26 da suka tsere zuwa wasu kasashe. Masu binciken hukumar kula da 'yan gudun hijira, sun danganta yawan kauran da matsanancin yanayi, kuma akwai yiwuwar yawan masu kauran ya karu.