1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A karo na biyu hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ɗage zaɓukan 'yan majalisun dokokin ƙasar

April 2, 2011

Tun bayan ɗage zaɓukan karo na farko, shugaban hukumar INEC Farfesa Jega ya nemi afuwar 'yan ƙasar dangane da ɗage zaɓukan majalisun dokokin Najeriyar.

https://p.dw.com/p/10mW9
Rumfar zaɓe a NajeriyaHoto: DW/Thomas Moesch

Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya INEC ta sanar da sake ɗage zaɓukan majalisun dokoki na wakilai da kuma dattijai waɗanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar ɗin nan da mako guda. Wato yanzu sai a ranar tara ga watannan na Afrilu za a gudanar da zaɓen wanda hakan ya haddasa ɗage sauran zaɓukan na shugaban ƙasa da na gwamnonin jihohi. Shugaban hukumar zaɓen Farfesa Attahiru Jega yace sun ɗauki wannan mataki ne bayan taron da suka gudanar da jam'iyun siyasar ƙasar a birnin Abuja. Tun a ranar Asabar ɗin nan ce hukumar ta ce ya zama dole a ɗage zaɓen 'yan majalisar dokokin tarayyar saboda rashin isowar wasu muhimman kayayyakin zaɓe. Jega wanda ya nemi afuwa da kuma haɗin kan 'yan Najeriya ya baiyana fatan gudanar da zaɓukan cikin nasara.

Zaɓen na majalisun dokoki na zama zakaran gwajin dafi na gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasar ta Najeriya wadda ke zama ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka. Hukumar zaɓen ta INEC ta ɗauki tsauraran matakai domin tabbatar da cewa an rage matsalar maguɗi da aka daɗe ana fama da shi a zaɓɓukan ƙasar.

Ana iya sauraron sautin rahotannin da muka tanadar muku game da ɗage zaɓukan idan aka duba daga ƙasa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal