A Kenya an fara jana'izar wadanda suka rasu a Garissa
April 10, 2015Rahotanni daga Nairobi babban birnin kasar na cewa daruruwan dalibai ne suka yi dafifi don yin ban kwana da takwarorinsu da mayakan suka halaka. Sai dai wasu bayanani sun ce har i zuwa wannan lokacin akwai wadansu iyaye da basu kaiga karbar gawarwakin 'ya'yansu ba.
Kafafen watsa labaran cikin kasar kuwa a daya hannun, na nuna tababa kan yawan daliban 142 da wasu jami'an tsaro da gwamnatin ke cewa su ne suka mutu, saboda har zuwa wannan lokacin, akwai karin wasu da ba a gansu ba, abin da gwamnatin ta musanta da kakkausar lafazi.
A jiya Alhamis ne dai shugaban kasar Uhuru Kenyatta, ya sanya hannu kan takardar ta'aziyya ga iyalan daukacin daliban da harin ya ritsa da su, yana mai cewa a matsayinsu na al'uma guda, ba zasu taba mantuwa da wadannan daliban ba.