1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau kasashe 6 suke komawa tattauna nukiliya na Koriya ta arewa

February 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuSD

Nan gaba a yau ne ake sa ran komawa teburuin tattaunawar kasahe 6 akan batun nukiliya na Koriya ta arewa.

Jamian kasashen Koriya guda biyu da Japan da Amurka da Rasha da kuma China sun shirya ganawa a birnin Beijing na kasar China domin ci gaba da tattaunawa akan wannan batu.

Ita dai koriya ta arewan ta ce a shirye take ta tattauna matakin farko game da batun dakatar da shirinta na nukiliya..

Rahotanni sunce mai yiwu ne a wannan karo Koriya ta arewa ta amince da rufe babbar tasharta ta nukiliya tare da barin supetoci kasa da kasa su kai ziyara tashoshin nata a madadin taimakon makamashi daga manyan kasashe duniya.

Sai dai wakilin Koriya ta arewa wajen tattanawar Kim Kye gwan yace mataki da Koriyan zata dauka wajen tattaunawar ta yau ya dogara akan matsayin da Amurka ta dauka.