1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ƙasar Kenya an sace masu aikin agaji

October 13, 2011

Hukumomi a ƙasar Kenya sun sanar da cewa an sace wasu ma'aikata dake bada agaji a sansanin yan gudun hijiran Somaliya a kan iyakar ƙasashen biyu

https://p.dw.com/p/12raR
'Yan gudun hijran Somaliya a sansaninsu na ƙasar Kenya dake yankin DadaabHoto: Picture-Alliance/dpa

A ƙasar Kenya jami'an tsaro suka ce an sace likitoci hudu dake aikin agaji a sansanin 'yan gudun hijara na Somaliya dake iyakar Kenya da Somaliya. Sifeto janar na yan sandan Kenya Leo Nyongesa yace jami'ai sun shiga farauta maharan ta sama da ta ƙasa, kuma kawo yanzu an rufe sansanin yan gudun hijaran wanda shine sanin yan gudun hijira mafi girma a duniya. Shugaban yan gudun hijira a sanin Dadaab, yace biyu daga cikin mutanen da aka sacen turawane dake aikin da ƙungiyar agaji ta Doctors Withiout Boaders, biyu kuma yan ƙasar Kenya ne. Kakakiyar Doktors Without Boaders tace kawo yanzu ba za ta iya tabbatar da labarin ba. Sace mutanen a yau ya biyo bayan sace turawa biyu a jiya, daya dan ƙasar Birtaniya da ba Faranshe, a wurin shakatawa a ƙasar Kenya dake kan iyakarsu da Somaliya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

AP