1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abba Ibrahim ya zama sabon sarkin kokawa na Nijar

Suleiman Babayo MAB
December 30, 2024

Jamhuriyar Nijar ta yi sabon sarkin kokawar gargajiya mai suna Abba Ibrahim wanda ya fito daga Yamai babban birnin kasar, lamarin da ya kawo karshen tasirin Kadri Abdou na Dosso da ake kira "Issaka-Issaka",

https://p.dw.com/p/4ogjB
Tutar Jamhuriyar Nijar
Tutar Jamhuriyar NijarHoto: Steve Allen/PantherMedia/IMAGO

A ranar Lahadf 29.12.2024 ne aka kawo karshen kokawar gargajiya a karo na 45  a garin Dosso na jamhuriyar Nijar. A bana, dan kokawa Abba Ibrahim na Niamey ne ya yi nasarar zama zakaran gwajin dafi inda ya ka da Kadri Abdou na Dosso.

Kasashen da suka samun tikitin shiga CHAN

A wasannin da aka kara na neman zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka na 'yan wasa da ke bugawa a gida, Najeriya ta samu galaba kan kasar Ghana da 3-1. Sannan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta doke Kamaru a gida 2 da 1. Ita kuma Senegal ta doke Laberiya da 2-0. Ita ma Ruwanda ta doke Sudan ta Kudu da 2- 1. Guinea ta bi Guinea Bissau har gida ta doke ta da 2- 1. Kana, an soke wasan da aka tsara tsakanin kasashen Zambiya da Mozambik, saboda tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka gudanar a kasar ta Mozambik.

Milan AC ta kori koci Paulo Fonseca

Rashin tabuka abin kirki na 'yan wasa, ya sa AC Milan koran kocinta Paulo Fonseca
Rashin tabuka abin kirki na 'yan wasa, ya sa AC Milan koran kocinta Paulo FonsecaHoto: LaPresse/IMAGO

A wasan kwararru na Italiya da ake kira Serie A, kungiyar AC Milan ta fatattaki mai horas da 'yan wasan kungiyar Paulo Fonseca bayan ya shafe watanni shida kacal kan mukamunsa, bayan da ya gaza samar da cikekkekiyar makoma ga kungiyar. A karshen makon da ya gabata kungiyar AC ta tashi 1 da 1 lokacin wasa da kungiyar AS Roma wadda ita kanta take can kasa a wasannin na Serie A da ke wakana a kasar Italiya. Kafofin yada labaran kasar ta Italiya sun ruwaito cewa Sergio Conceicao da ke zama tsohon mai horas da kungiyar Porto, shi ne zai karbi ragamar tafiyar da kungiyar ta AC Milan.

Wainar da aka toya a Premier League

A Premer League da ke ingila, Tottenham ta tashi 1 da 1 da kungiyar Wolverhampton, kana Crystal Palace ta doke FC Southhampton da 2- 1, yayin da Nottingham ta bi Everton har gida ta doke ta da 2-0. A nata bangaren, kungiyar Liverpool ta yi tattaki har gida ta yi wa West Ham cin kacar tsohon keke rankacau da 5-0. Sai dai mai tsaron baya na kungiyar ta Liverpool, Joe Gomez  ya samu raunin da mai yuwuwa zai shafe wani lokaci bai yi wasa ba.

Tennis da formula1 sun dauki hankali

Gasar neman cin kofin United ta fara daukar hankali a fagen tennis
Gasar neman cin kofin United ta fara daukar hankali a fagen tennisHoto: ALAIN JOCARD/AFP via Getty Images

A wasan Tennis, Dominant Rybakina ta jagoranci kasar Kazakhstan zuwa wasan kusa da na kusa da na karshe a gasar neman cin kofin United, bayan tawogar kasar Girka. A wasan tseren motoci na Formula One kuwa, Yuki Tsunoda zai wakilci tawogar motocin Bulls a shekara mai zuwa. Tsunoda mai shekaru 24 da haihuwa yana shekarunsa na biyar da tawogar Red Bulls.