1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abdoulaye wade ya samu lambar yabo ta Unesco

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/Buy5

Yau ne a birnin Paris na kasar France hukumar kulla da ilimi al´adu da kimiya ta Majalisar Ɗinkin Dunia, wato UNESCO, ta miƙa lambar yabo ga shugaban ƙasar Senegal Abdulaye wade.

Wannan shine karo na 2, da wani ɗan nahiyar Afrika, ya samu wannan lambar girmamawa, mai ɗauke da sunan Felix Houphouet Boigny, tsofan shugaban ƙasar Cote d´Ivoire .

Unesco, ta zaɓi Abdulaye wade, a sakamakon kyaukayawar rawar da ya taka, ta fannin kwantar da rigingimu a nahiyar Afrika , da kuma shinfiɗa ingantatar demokradiya a ƙasar Senegal.

Wannan buki, ya samu halartar shugabanin ƙasashe 7 na Afrika, da su ka haɗa da Olesegun Obasanjo na taraya Nigeria, da Amadu Tumani Ture na Mali, da kuma Jakaya Kikwete, na Tanzania, wanda a karo na farko, ya sadu da shugaba Jaques Chirac, tun bayan da hau wannan muƙami a watan desember da ya gabata.

Saidai Jam´iyun adawa a ƙasar Senegal, sun watsi da goran gayata, tare da danganta Abdulaye Wade, a matsayi wanda bai cencenta, ya samu wannan kauta ba.

A yayin da ya ke tantanawa tare da shugabanin 8, na Afrika Jaques Chirac, ya alkawarta masu cewar, za shi yi iya ƙoƙarin sa, domin saka batun tattalin arzikin ƙasashen Afrika a taron ƙoli na ƙasashen G8, da za ayi, a watan July na wannan shekara, a birnin Saint Petesburg, na ƙasar Rasha.