Abu Dhabi: Tausayawa Katar zai kai 'yan kasa kaso
June 7, 2017Talla
Kasar Daular Larabawa ta UAE ta hana mutane duk wasu kalamai na nuna tausayarsu ga kasar Katar don an mayar da ita saniyar ware, kuma a cewar mahukuntan kasar duk wanda aka samu da laifi zai iya fiskantar tsarewa a gidan kaso tsawon shekaru goma sha biyar kamar yadda kafar yada labarai ta Gulf News da ke da sansani a Abu Dhabi da ma tashar Al-Arabiya suka bayyana a wannan rana ta Laraba.
Daular Larabawan mai birnin Dubai tare da wasu kasashe manya a tsakanin kasashen Larabawa sun mayar da Katar gefe a harkokinsu na kasashen da ke a yankin Gulf a ranar Litinin bisa zargin tallafa wa ayyuka na ta'addanci. Zargin da tuni mahukuntan na Katar suka yi fatali da shi. Shugaba Erdogan na Turkiya dai ya ce kasashen su sake tunani.