1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Mata na fuskantar cin zarafi a Ghana

November 15, 2021

Rayuwar mata a Ghana ta kasance da wahala inda sotari ake samun maza da kan ci zarafin matansu ko 'yan matansu ta hanyar aikata kisan kai.

https://p.dw.com/p/430x5
Afrika Ghana Frauen reden über häusliche Gewalt - ein Tabu-Thema
Hoto: DW/M.Suuk

Kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewar akalla mata miliyan 736 ne ke cikin wani hali na cin zarafi inda kaso 30 daga cikin 'yan shekaru 15 ne da 'yan kai wanda kan danganci matsaloli na jima’i, muzgunawa ko kuwa duka. A Kasar Ghana abin ya wuce nan, inda rahotanni ke kara yawaita a kan mazaje wadanda ake zargi da kisan matan su. Hukumar 'yan sanda a Ghana ta dau rahotanni 306 na samari da ya kashe budurwarsa ko miji ya kashe matarsa.Lamarin da gwamnatin ta kara daukar mataki a kan wadanda aka samu da laifin cin zarafin matan.

Daga kasa za a iya sauraron sautin shirin