1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abuja: 'Yan Shi'a sun sake zanga-zanga

Ahmed Salisu
July 23, 2019

An sake samun arangama tsakanin 'yan Shi'a da jami'an tsaro a Abuja fadar gwamnatin Najeriya daidai lokacin da suka sake fitowa don yin zanga-zangar neman sakin shugabansu Sheikh Inrahim al-Zakzaky.

https://p.dw.com/p/3Mcyf
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Rahotanni daga Najeriya na cewa mabiya tafarkin Shi'a a Abuja fadar gwamnatin aksar sun sake yin arangama da jami'an tsaro a a rana ta biyu ta zanga-zangar da suke yi don yin matsin lamba ga hukumomin kasar kan su saki jagoransu Sheikh Ibrahim al-Zakzaky.

Masu aiko da rahotanni suka ce sojoji da 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a yunkurinsu na tarwatsa 'yan Shi'ar sannan daga bisani an ji harbe-harben bindiga an kama wasu daga cikinsu.

Ya zuwa yanzu dai ba wani labari da muka samu na asarar da aka samu a arangamar ta yau sai dai a jiya mutum shidda daga bangaren 'yan Shi'ar sun rasu baya ga wani babban jami'in 'yan sanda da wani dan jarida da kuma mai yi wa kasa hidima.