Adama Barrow zababben al'ummar Gambiya a 2016
January 9, 2017Farkon rayuwa da karatu
Shi dai Barrow an haife shi a ranar 16 ga watan Fabrairu na 1965 a Mankaman Kunda, wani karamin kauye na Jimara kusa da garin Basse mai makwabtaka da kogin Gambiya, ya yi makarantar firamare ta Koba Kunda da sakadaren Crab Island a birnin Banjul kafin daga bisani ya samu tallafin karo karatu ya je makarantar Muslim High School, bayan kammala wannan makaranta ya yi aiki da wani kamfani mai zaman kansa kafin daga bisani ya tafi birnin London na Birtaniya, ya yi karantu a fannin da ya shafi harkar gidaje da filaye a farkon shekarun 2000 a lokacin da ya ke karatu ya na kuma aiki da wani babban kantin siyar da kayayyaki na Argos a matsayin jami'in tsaro dan samun kudade ya dauki nauyin karatun da ya ke yi.
Barrow ya koma gida Gambiya bayan kammala karatunsa, a shekarar 2016 inda ya kafa kamfanin hada-hadar gidaje da filaye na Majum Real Estate ya zama baban shugaban kamfanin.
Idan muka koma bangaren siyasa a shekarar 2016 kawancen jam'iyyun siyasa suka zabi Barrow dan ya yi musu takara ta shugabancin kasar ta Gambiya , Kafin dai wannan lokaci bai taba rike wani babban mukami na siyasa ba, baya ga rike ma'ajin jam'iyyar UDP daya cikin jam'iyyun adawa a Gambiya.
A ranar daya ga watan Disambar bara ne dai al'ummar kasar ta Gambiya suka fita kada kuri'a a zaben da ya zama zakaran gwaji na gwada karfin ‘yan adawa a kasar, ya kuma zama zaben da sakamakonsa ya ba wa Shugaba Yahya Jammeh shan kayi, wani abu da ake ganin ya bude babi na sabuwar gwamnati a kasar bayan shekaru 22 da Shugaba Jammeh ya yi ya na mulki a wannan kasa .
Da fari dai Shugaban ya nuna alama ta amincewa da shan ka yi abin ya zamo abin mamaki musamman ga kasashen Yammacin duniya da ke masa kallon dan kama karya, sai dai ba aje ko'ina ba shugaban ya yi kwana da kalamansa inda ya ce bai yadda da sakamakon ba, dan haka ya nemi a sake komawa akwatin kada kuri'a , baya ga bayyana shirinsa na kalubalantar sakamakon zaben a kotu.
A lokacin takarar zaben dai na Gambiya Barrow ya yi alkawari na sake mayar da kasar cikin kungiyar kasashe masu magana da harshen Ingilishi ta Kwamanwel da mutunta tsare-tsare na kotun kasa da kasa mai hukunta masu manyan laifuka ICC ya kuma yi alkawari na samar da sauyi a tsarin tsaron kasar ta Gambiya in da ya ce zai kokari ya ga sun nesanta da harkokin siyasa.
Rayuwar cikin gida
A harkokin da suka shafi gida kuwa Barrow na da mata ne guda biyu da yara biyar, ya kuma kasance Musulmi mai bin tafarkin Sunnah, ya na kuma son kulob din Arsenal idan ana magana ta fuskar wasanni.
Nasaba ta kabila
Ya fito daga kabilar Fula wacce jam'iyyar UDP ke cewa su ne na biyu mafiya girma cikin kabilun Gambiya , wasu rahotanni n kuma na cewa dan Mandika ne kabila ta farko kuma ita ce kabilar mahaifinsa, mahaifiyarsa Fula. Ya dai girma ya na magana da harshen Fula kuma matansa biyu ma duk 'yan kabilar ta Fula ne.