Adawa da makamashin nukiliya a Japan
July 29, 2012Dubun dubatan masu zanga-zanga waɗanda suke ɗauke da wutar kandir da ƙananan fitillu sun yiwa majalisar dokokin Japan zobe, a wani mataki na nuna adawa da makamashin nukiliya bayan bala'in da ya afku a tashar Fukushima bara.
Kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP ya ce aƙalla mutane dubu 10 suka halarci zanga-zangar suna sanyen da taguwa mai kama da irin na 'yan sama jannati.
Daga farko dai masu zanga-zangar sun gudanar da wani jerin gwano inda suka ɗaga kwalaye masu ɗauke da gargadi kan lahanin da makashin ka iya sake janyowa ga al'umma.
Wannan zanga-zanga na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da wani rahoton da gwamnati ta fitar kan rikicin makamashin na bara ya nuna cewa jami'an gwamnati da wasu ma'aikatar kamfanin wutar lantarkin ƙasar na TEPCO sun yi sakaci sosai wajen ɗaukan matakan kariya daga afkuwar hatsari.
To sai dai Kamfanin wutar ya wanke kansa inda ya ce ƙarfin girgizar ƙasar da ta janyo wannan bala'in ya wuce tsammani bare kowani irin mataki na kariya.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu