AES na shure-shure kan barazanar tsaro daga ketare
December 23, 2024Cikin sanarwar de shugabannin Kasashen na AES suka fitar, suka ce sun lura cewa tun lokacin da suka dauki mataki na hadin kai domin ciyar da yankunansu gaba ta hanyar samun cikakken 'yancin tafiyar da lamuransu ba tare da shisshigi na wata kasa ta waje ba, Faransa ke ganin cewar suna barazana ga muradunta. Suka ce sun gano cewa tare da goyon bayan shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka da dama, kasar ta Farsansa da ta yi wa wadannan kasashe uku wato Nijar da Mali da Burkina Faso mulkin mallaka, na kokarin dakatar da wannan yunkurinsu na 'yantar da al'umomin yankin na AES, duk kuwa da cewa sun nanata cewar ficewarsu daga ECOWAS babu gudu babu ja da baya.
Karin bayani: Martanin 'yan NIjar kan ficewar AES daga ECOWAS
Sai sanarwar shugabannin na AES ta ce sun yi mamakin ganin karin watanni shida da ECOWAS ta bayar da zummar ci gaba da tattaunawa karin wa'adi, inda suka ce wata manakisa ce ta kasar Faransa domin ci gaba da aiwatar da matakan da ta dauka na neman wargaza wannan gamayya ta hanyar tayar da zaune tsaye. Szka ce, a cikin kungiyar ECOWAS, wasu tsirarun shugabanni ne ke fara aiwatar da ayyukan tada zaune tsaye a kai a kai, wadanda suka kasance 'yan kanzagi da kasashe na ketare ke bi domin hana ruwa gudu a cikin gamayyar kasashen na AES.
Karin bayani: Shekara da kafa AES
Sanarwar ta kawancen kasashen na Sahel ta kara da cewa, duk karin da kasashen AES ke yi na magance matsalolin ta'addanci a yankin baki daya, ba shi ne abin da ya kamata a ce sun yi farin ciki da shi ba, amma sun yarda su zama madogara ta tayar da hankalin kasashen na AES, ta hanyar sake farfado da 'yan tadda a yankin tafkin Chadi da ke yankin Sahel, da kuma a wasu iyakokin kasashe kaman na Nijar da Najeriya da Nijar da Burkina Faso, da kuma Benin da Burkina Faso inda ake b asu kayan yaki domin tayar da zaune tsaye a kasashen AES. A saboda haka ne kasashen uku na Nijar da Mali da Burkina Faso suka saka sojojinsu cikin shirin ko ta-kwana domin tunkarar wannan barazana da kuma kawo karshenta.