Ganawar gwamnati da tawagar Taliban
April 3, 2020Tun bayan isowar 'yan Taliban birnin Kabul a ranar Talatar da ta gabata dai, bangarorin sun gana sau biyu ta hanyar bidiyo. Tuni dai kafofin yada labaran Afganistan din suka sanar da cikakkun bayanai dangane da shirin musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu. Gwamnati za ta saki fursononi 100 na Taliban, a mamdadin jami'an sojojinta guda 20 daga kurkukun Taliban. Sai dai batun siyasa ba ya cikin ganawar.
Taliban dai na saka ran a sako mata mutanenta wajen 5,000 wadanda ke garkame a kurkukun gwamnatin Afganistan. Da fari dai shugaba Ashraf Ghani ya yi watsi da wannan bukata, sai daga bisani ya amince da sakin mayakan na Taliban kadan-kadan, a wani mataki na ganin cewar kasarsa ta samu zaman lafiya.
Hadin kai saboda Coronavirus
Sai dai har yanzu babu bayani dangane da ko yaushe za a fara tattaunawar gwamnatin cikin gida, kasancewar 'yan Taliban din sun ki amincewa da tawagar da gwamnati ta nada domin wakitarta a zaman. To sai dai yanzu gwamnatin Afganistan din da bangaren Taliban din nada abokin gaba daya, wata cutar Coronavirus, wadda ke ci gaba da yaduwa a kasar.
Tuni dai Taliban din ta amince da matakan bayar da goyon bayanta wajen yakar cutar, ta wani gangami na bidiyo da ta yada a shafinta na Twitter. A hirarsa da kamfanin dillancin labaran AP, kakakin Taliban Sabihullah Mudschahed ya bayyana cewar, idan har cutar ta bulla a yankunan da ke karkashin ikonsu, to ko shakka babu zasu dakatar da fada.
Fursinoni sun shaki iskar 'yanci
A wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a gidajen yarin kasar dai, a farkon wannan makon ne hukumomin Afganistan din suka saki daruruwan fursunoni da suka aikata miyagun laifuka, sai dai babu na Taliban da wasu masu laifukan ta'addanci. A hukumance dai, a yanzu haka akwai mutane wajen 180 da suka kamu da COVID-19, kuma tuni wasu hudu suka rasa rayukansu.