1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan na sulhu da Taliban

Abdul-raheem Hassan
September 12, 2020

Gwamnatin Afganistan ta fara tattauna kulla yarjejeniyar zaman lafiya da mayakan Taliban da zai kawo karshen zubar da jini tsawon shekaru 40.

https://p.dw.com/p/3iMsA
Katar Doha | Afghanistan Friedensverhandlungen | Abbas Stanikzai
Hoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

Cimma wannan yarjejeniya na cikin manyan kudororin gwamnatin Shugaba Aschraf Ghani domin tabbatar da zaman lafiya a kasar Afganistan, sai dai har yanzu bangaren mayakan Taliban ba su fayyace bukatunsu kan yarjejeniyar gaba daya ba, amma kwamitin sulhu da ya hada da ya samu halartar sakataren gwamnatin Amirka Mike Pompeo na fatan za a cimma matsaya kan bukatun kowa.

A wata kwarya-kwaryar sulhu da Amirka ta shiga tsakanin bangarorin biyu a baya-bayannan, an cimma yarjejeniya na yin musanyar fursunoni tsakanin Taliban da gwamnati, matakin da ya kai ga Taliban amincewa da tattaunawar zaman lafiyar da aka fara.