1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban sun tsagaita wuta a Afganistan

Abdullahi Tanko Bala GAT
May 25, 2020

A kasar Afganistan kungiyar Taliban ta tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku domin bai wa Musulmi damar gudanar da shagulgulan sallah bayan kammala azumin watan Ramadana.

https://p.dw.com/p/3cjxe
Afghanistan Maulvi Niaz Mohammad Taliban
Hoto: picture-alliance/AP Images/R. Gul

Jama'a suin yi ta gudanar da karatun alkur'ani da addu'o'i a Afghanistan sabanin karar harbe-harben bindigogi a sassan kasar lokacin da suka samun wannan labari a jajibirin sallar. A ranar sallar Musulmi da dama sun sami zuwa masallaci ba tare da wata fargaba ko tashin hankali ba. Sayed Sulaiman na daya daga cikin masallata da suka bayyana gamsuwa da tsagaita wutar:

Ya ce "Hakika tsagaita wutar ta zo a daidai lokacin da ya dace. Ina fata wannan zai zama farkon samun dorewar zaman lafiya a kasar baki daya."

 

Shi ma shugaban Afghanistan Asharaf Ghani ya yi maraba da tsagaita wutar yayin wani taron manema labarai da ya kira. Sai dai kuma bai saki jiki ba, yana taka tsan-tsan.

Ya ce "Na umarci dukkan sojojinmu su sa ido sosai a kan tsagaita wutar, su kuma kasance cikin shirin ko-ta-kwana. To amma domin samun zaman lafiya mai dorewa muna bukatar tattaunawa da juna. Kuma gwamnatin Afghanistan a shirye ta ke ta yi hakan."

Afghanistan Eid Fest Zuckerfest in Khost
Hoto: DW/F. Zaher

Makonni biyu da suka wuce shugaba Ashraf Ghani ya sanar da cewa zai ci gaba da kai hari a kan 'yan Taliban sakamakon wasu hare-hare biyu masu ta da hankali da aka kai kan wani ayarin jama'a a makabarta a gabashin kasar wanda ya hallaka mutane 32. Hakan nan kuma maharan sun kai farmaki wani asibiti a birnin Kabul inda suka kashe wasu iyaye mata matasa da ba su jima da haihuwa ba. Jarirai biyu sun mutu a sakamakon harin yayin da wasu kuma suka rasu suna rungume a hannun iyayensu mata. Gwamnatin Afghanistan ta dora alhakin harin a kan 'yanTaliban, sai dai kungiyar wadda ita ma ta yi Allah wadai da harin ta ce ba ta da hannu a wannan harin.A karshen watan Fabrairu ne dai Amirka da Taliban suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniya wadda ya kamata ta kawo zaman lafiya a Afghanistan. Tun daga lokacin da aka sanya hannu a kan yarjejeniyar, 'yan Taliban sun kai hare-hare fiye da sau 3800 a cewar gwamnatin Afghanistan, hare-haren da ta ce sun hallaka jama'a fararen hula fiye da 400.

Afghanistan Eid Fest Zuckerfest in Khost
Hoto: DW/F. Zaher

Dukkan bangarorin biyu dai na gwamnatin Afghanistan da kuma Taliban sun yi musayar fursunoni a 'yan makonnin da suka gabata. Wannan na daga cikin sharuddan da bangarorin biyu suka gindaya kafin zama domin tattauna yiwuwar samun zaman lafiya a Afghanistan. Ko da yake 'yan Afghanistan ba za su tsammaci hare-haren bamabamai ko wasu farmaki a cikin kwanaki uku na bukukuwan sallah ba, Musulmi a kasar har yanzu suna bakin ciki da abin da ke faruwa cewar Naveed Osmani wani mazaunin Kabul:

Ya ce "Muna kewaye da jami'an tsaro sannan ga talauci da ya yi mana katutu, yanzu kuma ga cutar Corona na yaduwa. Mun yi addu'a a masallatai Allah ya kawar mana da wannan cuta daga Afghanistan."

 A hukumance dai mutane kusan dubu 10 ne suka kamu da Corona a kasar yayin da wasu 200 kuma suka rasu a sakamakon cutar a fadin kasar. Tun dai bayan da Amirka ta mamaye Afghanistan tare da hadin gwiwa da sojojin kasa da kasa a shekarar 2001 ake kulla yarjeniyoyi na tsagaita wuta, yayin da a waje guda ake kokarin lalubo hanyoyin da za a kawo karshen rikicin baki daya. Shekaru biyu da suka gabata ma an yi irin wannan yarjejeniya a lokacin sallah karama amma 'yan Taliban suka cigaba da kai hari kwanaki uku bayan tsagaita wutar.