1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Amirka za su fita Afganistan

Abdul-raheem Hassan
October 8, 2020

Kungiyar Taliban ta yi maraba da matakin Amirka na janye sauran sojojinta da suka rage a cikin kasar Afghanistan, Shugaba Donald Trump ya ce matakin zai tabbata kamin karshen shekarar 2020.

https://p.dw.com/p/3jd6W
Afghanistan 2017 | Operation Resolute Support | US-Armee
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Operation Resolute Support Headquarters/Sgt. Justin T. Updegraff

A shekarar 2001 sojojin Amirka suka shiga Afgansitan da zimmar yaki da kungiyar IS. 'Yan Taliban sun ce janye sojojin mataki ne mai kyau da zai tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da Amirkan a watan Febrairun 2020.

Shugaban Amirka Donald Trump ya sanar ta twitter cewa, "Sauran dakarun kasarsa da suka rage a Afganistan za su koma gida gabannin Kirsimeti" amma bai yi karin bayani ba.

Gwamnatin Afganistan ta ce a shirye ta ke ta murkushe duk wani hari daga 'yan adawa bayan ficewar dakarun Amirka daga kasar. Zuwa yanzu dai ba wani sojan kasar waje da mayakan Taliban suka kashe, tun bayan fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a watan Satumban 2020.