1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi wa wasu mayakan Taliban 900 afuwa

Binta Aliyu Zurmi
May 26, 2020

Mahukuntan a kasar Afganistan sun bukaci mayakan Taliban da su kara wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta a daidai lokacin da gwamnati ta sanar da shirinta na yin afuwa ga mayakan Taliban kimanin 900 da suke tsare da su.

https://p.dw.com/p/3cmQW
Pakistan Taliban-Führer Mullah Fazlullah
Hoto: picture-alliance/dpa/Ttp

Da yake jawabi ga manema labarai mai magana da yawun rundunar tsaron Afghanistan Javid Faisal, ya ce akwai matukar mahimmanci a kara wa'adin tsagaita wutar da ke karewa a yau, a wani mataki na kawo karshen zubar da jini.

A karshen watan Ramadana ne kungiyar ta Taliban ta sanar da tsagaita wuta domin samun damar gudanar da shagulgulan sallah. Hakan kuwa ya zo ne kwanaki kalilan bayan wakilin Amirka a shirin samar da zaman lafiya Afghanistan din Zalmay Khalilzad ya kai ziyara biranen Kabul da ma Doha na Daular Katar.