An kamo hanyar zaman lafiya
February 21, 2020A wannan Juma'ar, Amurka da bangaren Taliban da rundunar gwamnatin Afghanistan suka cimma matsaya kan dakatar da kai hare-hare kan juna a kasar Afghanistan. Mako guda ake son ganin an bi don mutunta wannan doka, wanda idan an yi nasara, sai a dora da yarjejeniyar da aka shata a can baya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ya fidda wannan sanarwar a shafinsa na tweeter, bai yi karin bayani kan manufar son ganin an rage hare-haren ba, sai dai ya ce manuniya ce a game da inda aka dosa a kokarin samar da zaman lafiya a kasar da aka kwashi sama da shekaru goma sha takwas ana fama da rikici.
A ranar ashirin da tara na wannan watan Febrairun da muke ciki, bangarorin za su rattaba hannu a hukumance a kan yarjejeniyar a birnin Doha, tuni Mista Pompeo ya shawarci bangaren Afghanistan da su yi amfani da wannan damar don ganin an cimma zaman lafiya na din-din.