1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta kai hari a Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 3, 2019

Hukumomi a Afghanistan sun nunar da cewa adadin wadanda suka hallaka sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai a kasar ya karu zuwa 16, yayin da wasu 119 suka jikkata.

https://p.dw.com/p/3Oulx
Afghanistan Explosion in Kabul
Harin ta'addanci a Afghanistan ya rutsa da mutane da damaHoto: picture-alliance/AP Photo/R. Gul

Rahotanni sun nunar da cewa harin wanda tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai shi, na zuwa ne jim kadan bayan da jakadan musamman na Amirka a Afghanistan din Zalmay Khalilzad ya yi wani taro da mamhukuntan kasar, da kuma aka yada a gidajen talabijin dangane da batun tattaunawar da suke kan yi da 'yan kungiyar ta Taliban, domin cimma yarjejeniyar da za ta kai ga ficewar kimanin sojojin Amirkan 5,000 daga kasar cikin watanni biyar. Wannan hari dai an kai shi a wani waje da ake kira da "Green Villege" inda mafi akasari ofisoshin kungiyoyin bayar da agaji da kuma na jakadanci kasashen waje suke. Dama dai "Green Villege" ya saba da fuskantar munanan hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Taliban.