1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta hana zanga-zanga a Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 9, 2021

Rahotanni daga Afghanistan, na nuni da cewar gwamantin mayakan kungiyar Taliban ta haramta zanga-zanga a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/407v3
Afghanistan Kabul | Anti-Pakistan Proteste
Taliban ta haramta zanga-zanga a AfghanistanHoto: WANA/REUTERS

Cikin wata sanarwa da ke zaman ta farko tun bayan kafa gawamnatin da Taliban, ma'aikatar cikin gida ta kasar Afghanistan din ta nunar da cewa akwai tsattsauran hukunci ga duk wanda ya saba dokar haramta zanga-zangar. Dubban 'yan kasar ta Afghanistan dai sun yi ta gudanar da zanga-zanga a 'yan kwanakin nan, suna masu neman samun 'yanci da bayar da 'yanci ga mata da kuma kyamar bakin da Pakistan ke tsomawa a harkokin kasar. A hannu guda kuma kungiyar Taliban din ta dauki mataki a kan matan kasar, inda a yanzu aka hana su zuwa aiki kana ba za a kara biyansu albashi ba, kamar yadda wadanda abin ya shafa suka shaidar.