1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambliya ta halaka mutane a Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 29, 2021

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa mutane 150 sun rasa rayukansu, sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta afku a gundumar Nuristan da ke yankin Arewa maso Gabashin Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3yI4Z
Afghanistan | Hochwasser Überschwemmung
Ambaliyar ruwa ta halaka mutane da dama a AfghanistanHoto: Reuters/M. P. Hossain

Mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar da hakan, sai dai bai yi wani karin haske ba. Kakakin gwamnatin gundumar ta Nuristan mai cike da tsaunuka Mohammad Sayed Mohmand ya shaidar da cewa, mamakon ruwan saman ya lalata kimanin gidaje 100 a kauyen Terdesh tare da halaka mutane 60, sai dai ya ce adadin wadanda suka rasa rayukan nasu ka iya karuwa. Kungiyar Taliban din ce dai ke iko da mafi yawa daga yankunana gudnumar ta Nuristan, abin da ya sanya gwamnatin yankin ke kira ga kungiyar da ta bayar da dama ga masu aikin ceto domin kai daukin gaggawa.

Taliban din dai na rike da kusan rabin kasar ta Afghanistan, kuma tun bayan ayyana janyewar sojojin Amirka da na kungiyar tsaro ta NATO take kara mamaye wasu yankunan kasar. A hannu guda kuma sakataren harkokin kasashen ketare na Amirkan Antony Blinken ya bayyana cewa, a shirye Washington take ta taimaka tare da kwashe jami'an da suka taimakawa sojojinta yayin zamansu na shekaru 20 a Afghanistan din. Rahotanni sun nunar da cewa mafi akasarin wadanda suka yi wa sojojin Amirkan tafinta da iyalansu, na fuskantar barazan daga Taliban din a yanzu haka.