Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka
August 7, 2020Za mu yaye kallabin shirin na wannan makon ne da labarin da jaridar die Tageszeitung ta rubuta mai taken: "An kashe 'yan gudun hijira a yayin da suke barci." Ta ci gaba da cewar a kalla mutane 18 aka kashe a wani hari da aka kai wa sansanin 'yan gudun hijirar da suka tsere daga gidajensu saboda rikicin Boko Haram a arewacin Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya. Harin da ya janyo sukan sojoji. A karshen makon da ya gabata ne dai, mayakan na Boko Haram suka sake kai hari Kamaru, a yankin da aka kebe domin bai wa mutanen da suka bar matsugunensu kariya daga hari.
Rahotanni na nuni da cewar, maharan sun saci jiki zuwa cikin kauyen da sanyin safiyar ranar Lahadi, lokacin da 'yan gudun hijirar ke bacci. Mazauna kauyen sun shaidar da cewa, maharan sun jefa wa gungun mutanen da ke barci gurneti, harin da ya halaka mutane 18 tare da jikkata wasu guda shida. Kimanin mutane 800 ne dai ke samun mafaka a sansanin da ke Nguetchéwé na gundumar Mayo-Moskota a yankin arewacin kasar ta Kamuru, a kan iyaka da Najeriya. Akwai 'yan gudun hijira daga Najeriya da yawansu ya kai dubu 116, da suka tsere Kamarun, saboda rikicin Boko Haram.
"Masu zanga-zangar adawa sun lashi takobin hambarar da shugaban Mali, biyo bayan gaza warware rikicin siyasar kasar." Da haka ne jaridar Neues Deutschland ta fara buga labarinta a kan halin da ake ciki dangane da zanga-zangar neman sauyi a wannan kasa ta yammacin Afirka. Jaridar ta ci gaba da cewa, tsawon makonni ke nan Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali, ke fuskantar gangamin nuna adawa da shi a fadin kasar. Kungiyar Bunkasa tattalin Arzikin Afirk ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta gaza warware wannan matsalar. Zanga-zangar ta ci gaba tun bayan yunkurin na ECOWAS.
Gamayyar 'yan adawa masu rajin kawo sauyi da ake kira M5-RFP, tun bayan kaddamar da gangamin a ranar biyar ga watan Yuni, na ci gaba da turjiya ga bukatar warware rikicin kasar, kamar yadda mai fafutuka Mohammed Diarra na jam'iyyar SADI ya ayyana. A wannan makon ma shugabannin kasashen yammacin Afirkan sun gaza shawo kan wannan matsala. A taro na musamman da suka yi, shugabannin sun gabatarwa 'yan adawar shirin kafa gwamnintin hadaka, amma a karkashin shugaba Keita tayin da suka ce a kai kasuwa.
A kasar Zimbabwe da ke yankin kudancin Afirka kuwa, fitattun mutane a cikin al'umma ne suka yi gangamin nuna adawa da yadda ake ci gaba da tursasa mutane a cewar jaridar die Tageszeitung. Gangamin mai taken "#ZimbabweanLivesMatter," ya kunshi 'yan siyasa da fitattun 'yan wasan kwallon kafa daga kasar Afirka ta Kudu da sauran kasashen da ke yankin, a matsayin goyon baya ga wadanda ake azabtarwa a Zimbabuwe.
Fafutukar "#BlackLivesMatter" da ta samo asali daga Amirka kuma ta bazu a duniya, ta fadada zuwa kan batun sace 'yan jarida da cin zarafin al'umma daga bangaren masu mulki da almundahana da dukiyar kasa. Fitattu daga cikin wadanda ke cikin fafutukar ta Zimbabuwe, sun kunshi zababben shugaban Malawi Lazarus Chakwera da dan kwallon Ingila mai asali da Afirka ta Kudu Percy Tau da fitattcen shugaban adawa a Afirka ta Kudu Julius Malema da Mmusi Maimane.