1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
April 24, 2020

Har yanzu dai annobar Coronavirus na ci gaba da daukar hankalin jaridun na Jamus, a labaran da suke bugawa kan nahiyarmu ta Afirka.

https://p.dw.com/p/3bM9X
Südafrika Corona-Pandemie Soldaten
Jami'an tsaro na sintiri domin tabbatar da bin dokar zaman gidaHoto: picture-alliance/dpa/J. Delay

Za mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung, wadda ta ce sau da yawa matakan takaita fita da kulle da ake dauka a kasashen Afirka domin dakile yaduwar Coronavirus ba sa cimma buri. Ta ce kasashen Afirka da dama sun yi koyi da kasashen Turai a matakan da suke dauka na yaki da cutar ta COVID-19, amma yanayin rayuwa ya bambanta tsakanin nahiyoyin biyu. Jaridar ta ce abin da ya yi nasara a Turai yana iya rugujewa a Afirka. Ta ce mafi akasarin 'yan Afirka masu kananan aikin hannu ne da suka dogara da abin da suke samu yau da gobe domin rayuwa, wato 'yan hannu baka hannu kwarya ne, idan ba su fita aiki a rana ba to da wahala su sami abin sakawa bakin salati.

Rana zafi inuwa kuna

Ko da yake wajibi ne a dauki matakan hana fita domin kare lafiya da rayukan al'umma, amma ana bukatar yin duba da nazari mai zurfi ta yadda al'ummar ba za ta kara tsunduma mawuyacin hali sakamakon wadannan matakai na kulle a gida ba. Jaridar ta ce dole ne gwamnatoci a Afirka su tabbatar talakawa sun sami tallafi a wannan yanayi da aka shiga, in ba haka ba duk matakan da za a dauka ba za su cimma manufar da aka sa gaba ba.
A kasar Afirka ta Kudu kuwa dokar hana fitan sakamakon Corona ta kara tsananta rarrabuwar kai tsakanin al'umma, inji jaridar Neues Deutschland. Ta ce tun a ranar 27 ga watan Maris dokar killace jama'a domin hana yaduwar Coronavirus ke aiki a Afirka ta Kudu. Attajirai za su iya jurewa amma ga talaka dokar barazana ce ga rayuwarsa, kasancewa sai ya fita aiki ne zai sami abinci.

Malawi Markt Preissteigerung
Wasu sai sun fita su samu abinciHoto: Reuters/M. Hutchings

Ceton rai ko barazana?

Dokar dai kamar a kasashe da dama, ta yarda mutane su fita sayen muhimman abubuwa musamman kayan abinci ko asibiti. Afirka ta Kudu dai kasa ce da ake da babban gibi tsakanin attajirai da talakawa kuma dokar hana fitan ta fito da matsalar a fili. Jaridar ta ce ga talakawan kasar da akasari ke rayuwa a gidaje da ke cunkushe da jama'a, taken dokar da ke cewa zama a gida ceton rai, ka iya sauyawa ya zama babbar barazana ga rayuwa.

Somalia ruft Notstand aus wegen Heuschreckenplage
Farin dango na barazanaHoto: picture-alliance/dpa/AP/B. Curtis

Coronaviru hadi da farin dango babbar barazana ta yunwa, wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Tageszeitung ta buga. Ta ce a watannin baya- bayan nan, yankin gabashin Afirka ya yi fama da matsalar farin dango da suka lalata amfanin gona.

Yanzu kuma ga annobar Corona da za ta haddasa matsalar karancin abinci za kuma ta sa a sha wahala wajen yaki da farin dangon, kasancewar an rufe iyakokin kasashe babu zirga-zirga yayin da a lokaci guda ake fama da karancin magungunan feshi domin yaki da farin dangon, da yanzu za a shiga wani lokaci da suke kyankyasa. Bugu da kari a kudanci da tsakiyar kasar Somaliya, inda 'yan tawayen kungiyar al-Shabaab ke da fada a ji, babu yiwuwar yaki da farin dangon. Hatta kayakin tallafi ba sa kai wa ga mazauna yankunan. Wato ke nan ga matsalar farin dango ga annobar Coronavirus ga kuma matsalar rashin tsaro.