1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
March 27, 2020

Coronavirus a Afirka da siyasar kasar Guinea Conakry da salon mulkin Adama Barrow na Gambiya, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3a84l
Covid-19 Testing Coronavirus Berlin Deutschland
COVID-19 Karancin kayan gwaji da sauran kayan aiki a asibitocin AfirkaHoto: Getty Images/S. Gallup

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga labari mai taken an bar kowa ya yi ta kanshi dangane da cutar Corona a Afirka. Ta ce a birane da dama na nahiyar Afirka akwai cunkoson gidaje musamman a ire-iren unguwannin talakawa, inda mutane ke rayuwa a matse, babu kyawawan tsare-tsare na tsabta, sannan hanyoyin kiwon lafiya ma ba su da inganci. Yanzu da aka samu kai cikin wannan anoba ta Coronavirus, babu wasu kayayyaki na kariya da abubuwan taimaka wa numfashi. Jaridar ta ce saboda haka da yawa daga cikin kasashen Afirka ba su shirya ga annobar da ta addabi duniya ba.

Cutar COVID-19 ta fi tasiri ga tsofaffi

Abin da kawai zai iya taimakawa shi ne kasancewar daukacin al'ummar Afirka matasa ne, kuma bisa bayanai na masana kwayar cutar ta Coronavirus ba ta tasiri sosai kan matasa idan aka kwatanta da tsoffafi. A karshe jaridar ta yi wa al'ummar Afirka musamman ma masu harkar wakokin zamani jaje, bisa rasuwar shahararren mawakin nan dan kasar Kamaru Manu Dibango wanda Allah Ya yi wa rasuwa a kasar Faransa bayan ya kamu da cutar Covid-19. Dibango ya rasu yana da shekaru 86 a duniya. Ya dai shahara da wakarsa nan ta Mamako mamasa.

USA Alpha Condé, Präsident der Afrikanischen Union vor der UNO Vollversammlung
Shugaba Alpha Condé na Guinea ConakryHoto: Reuters/S. Stapleton

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Guinea Conakry tana mai cewa shugaban kasa Alpha Condé ya bari an gudanar da zabe. Ta ce zanga-zanga da tashe-tashen hankula ba su sa an dakatar da kuri'ar raba gardama da Shugaba Condé ke son ya yi amfani da wannan dama don tsawaita wa'adin mulkinsa ba.

Annobar Coronavirus ta shiga kasar

An ta dai dage lokacin gudanar da zaben, amma a karshen makon da ya gabata an yi zaben abin da ya ci karo da bullar annobar cutar Coronavirus a kasar. Condé  ya shafe shekara 10 a kan karagar mulki, bayan wasu shekaru gommai da ya yi a fagen siyasar kasar ta Guinea. 'Yan adawa sun zargi shugaban da makarkashiya ba kawai dangane da kuri'ar raba gardamar ba, sun ce an yi magudi a kundin rajistar masu zabe. 

Gambia Präsident Adama Barrow kündigt Wahrheitskommission an
Shugaban kasar Gambiya Adama BarrowHoto: picture-alliance/AP Photo

A karshe sai jaridar Neue Zürcher Zeitung da ta yi tsokaci kan salon mulkin shugaban kasar Gambiya Adama Barrow. Ta ce Gambiya ba ta rabu da mulkin kama karya ba, zababben shugaban kasa Barrow bai cika alkawurin da ya dauka na sauka daga karagar mulki bayan shekaru uku ba. Jaridar ta ce maimakon haka gwamnatin Gambiya na daukar matakan murkushe masu zanga-zangar neman sai shugaban ya cika alkawarinsa na sauka daga karagar mulki a 2020.

Gazawa wajen gudanar da mulki

Jaridar ta ci gaba da cewa an jima ana zargin Barrow da rashin iya shugabanci. Masu adawa na ganin zargin da suke masa ya tabbata gaskiya cewa matakan danniya da murkushe 'yan adawa da shugaban ke dauka sun yi kama da na tsohon shugaban mulkin kama karya Yahya Jammeh.