1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Umaru AliyuApril 10, 2015

Jaridun na Jamus a wannan mako sun yi sharhuna da dama, musamman game da zaben shugaban kasa a Najeriya da kuma harin 'yan ta'adda a kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/1F5vC
Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Presse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Jaridar Die Zeit ta yi sharhi game da zaben shugaban kasa a Tarayyar Najeriya da ya gudana lami-lafiya makonni biyu da suka wuce da kuma amincewar da shugaban da ya sha kaye, wato Goodluck Jonathan na amincewa da kayen da ya sha, ya kuma yi kira ga magoya bayansa su karbi wannan kaddara. Game da haka ne jaridr tace: Najeriya ta koyawa nahiyar Afirka darasi. Shugaba Goodluck Jonathan ya yi abin da ba al'ada bace ta yan Afrika, wato shugaban kasa ya yarda da kayen daya sha cikin ruwan sanyi. Hakan yana da muhimmanci saboda Najeriya, inji jaridar Die Zeit, ba kasa ce da yan mulkin kama karya a ko ina suke a Afrika za su yi watsi da wannan abu da tayi ba. Najeiya kasa ce dake da nauyin gaske a nahiyar Afirka, kuma tun daga ranar 28 ga watan Maris, darajarta ta kara daukaka a fagen ci gaban democradiya. Kafin zaben na shugaban kasa, duniya gaba daya ta dauka ranar 28 ga watan Maris, zata zama ranar da za ta kafa tushen wargajewar Najeriya, tattare da tashin hankali da asarar rayuka, amma sai gashi kasar ta baiwa marada kunya. Nan gaba idan shugabannin Najeriya suka fito suka zargi sauran shugabannin Afrika da laifin rashin kiyaye democradiya, suna da dalili mai karfi da izinin yin hakan.

Jaridar Tageszeitung ta tabo mummunan harin da 'yan ta'adda, da ake zaton 'yan kungiyar al-Shabaab na Somaliya ne suka kai garin nan mai suna Garissa na Kenya, inda a jami'ar dake garin suka halaka mutane akalla 150. Jaridar tace mummunan fushi da bakin ciki da zaman makoki ne suka mamaye makon Easter a kasar ta Kenya, sakamakon wannan hari na yan ta'adda. Jami'an tsaro da bangaren gwamnati gaba daya sun kasa yin wani bayani a game a yadda har wannan mummunan hari ya auku,ko da shike nan da nan bayan yinsa, mahukunta suka ce hakan bai wuce aikin 'yan kungiyar al-Shabaab ba, idan aka yi la'akari da irinsa da ta kai birnin Nairobi a shekara ta 2013, inda mutane da yawa suka mutu. Kungiyar ta al-Shabaab tana kaiwa kasar ta Kenya hare-hare ne domin adawa da kasancewar sojojin kasar a Somaliya, a matsyin wani bangare na rundunar hadin gwiwa na nahiyar Afirka dake yaki da aiyukan ta'adda a wannan kasa.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako ta maida hankali ne kan sanarwar Faransa na fito da takardun da suka kunshi bayanai game da ainihin abin da ya faru, lokacin kisan kare dangi da ya gudana a Rwanda a shekara ta 1994. Jaridar tace shekaru 21 bayan wannan kisa na kare dangi, inda akalla mutane 800.000 suka mutu yawancinsu yan kabilar Tutsi da 'yan hutu masu sassaucin ra'ayi, mahukunta a Faransa sun yanke shawarar fitar da takardun bayanan Hakan dai inji jaridar, ya biyo bayan kokarin Faransa ne na wanke kanta daga zargin cewar tana da hannu a wannan kisa na kare dangi da 'yan Hutu masu matsancin ra'ayi suka aikata a shekara ta 1994, jim kadan bayan kisan gilla da aka yiwa shugaban kasar ta Rwanda, Juvenal Habyarimana.

Frankreichs Präsident Hollande mit ruandischem Amtskollegen Kagame
Shugaba Paul Kagame na Rwanda da takwaran aikinsa na Faransa, Francoise HollandeHoto: A. Jocard/AFP/Getty Images

A karshe, jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi kan abin da ta kira, harajin tilas da yan Eritrea mazauna Jamus zasu rika biyan gwamnatin kasarsu, inda tace wannan harajin tilas, zai baiwa gwamnatin ta Eritrea, wadda gwamnati ce ta mulkin kama karya damar sayen makamai da za a yi amfani dasu domin ci gaba da gallazawa 'yan kasar. Shi dai wannan haraji na dole, 'yan Eritrea, ko yan gudun hijira ne da suka kuracewa kasar domin tsira da rayukansu, ko wadanda ke zaune a nan Jamus a yanayi na halaliya tilas su biya shi, duk irin munin halin da suke zaun ciki a wannan kasa. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace da alamu gwamnatin Jamus ta san da haka, kuma ta ki daukar wani mataki a kai, domin kuwa tun shekara ta 1995 gwamnatin ta Eritrea take tilastawa yan kasar dake zaune a Jamus su rika biyan irin wannan haraji na tilas.