1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Afirka ta Kudu ta amshi ragamar shugabancin G20

November 19, 2024

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce kasarsa za ta yi amfani da shugabancinta na G20 wajen bunkasa tattalin arziki da samar da abinci da kuma bunkasa ilmin kirkirarriyar basirar AI.

https://p.dw.com/p/4nAs4
Shugabannin kasashen duniya a taron G20 na birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil
Shugabannin kasashen duniya a taron G20 na birnin Rio de Janeiro na kasar BrazilHoto: Eric Lee/The New York Times/AP/picture alliance

Kasashen na G20 masu karfin tattalin arziki sun amince da shugabancin Afirka ta Kudu wacce kuma za ta jagoranci taron da kasashen zasu gudanar a nan gaba. Shugaba Ramaphosa ya ce wannan ne karon farko da Afirka zata karbi bakuncin taron na G20, inda ya ce zasu yi amfani wannan dama wajen tafiya da murya daya.

Karin bayani:An bude taron kungiyar G20 na bana 

Da yake jawabi yayin karkare taron na birnin Rio de Janeiro, shugaban kasar Brazil mai masaukin baki Luiz Inacio Lula da Silva ya bukaci kaashen da ke gurbata muhalli dasu yi duk mai yiwuwa wajen cimma rage makamashin iskar da ke gurbata muhalli.