1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka za ta iya ciyar da kanta da kanta

November 2, 2012

Sai dai yawan dogon turanci da shingayen ciniki da ƙasashen Afirka ke kakkafawa tsakaninsu ya na kawo ciƙas ga ƙoƙarin magance ƙarancin abinci a nahiyar.

https://p.dw.com/p/16bzo
Hoto: picture-alliance/dpa

To a yau za mu fara ne da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a babban labarinta mai taken „Yadda Afirka za ta iya taimakon kanta da kanta“ ta rawaito wani nazari da Bankin Duniya ya yi da ke cewa yawa-yawan dogon turanci da shingayen ciniki na hana manoman nahiyar Afirka taɓuka wani abin kirkiki idan aka kwatanta da takwarorinsu na wasu ƙasashe masu tasowa.

„Yayin da a shekarun bayan nan ƙasashen Afirka na kudu da Sahara ke samun bunƙasar tattalin arziki, amma ba haka abin ya ke ba a fannin aikin noma. Bisa nazarin na Bankin Duniya da dai Afirka za ta iya noma wa kanta kayan abincin da take buƙata, amma sau da yawa ƙasashen ne ke sanya wa kansu tarnaƙi, musamman yawan dogon turanci, da kafa shingayen ciniki tsakaninsu da yawan kuɗin kwasta ga kuma uwa uba yawan bincike a kan hanyoyin cikin gida wanda ke karya guiwar manoma, ya na kuma haddasa tashin farashin abinci ga mabuƙata. Bankin ya kaɗu da cewa har yanzu Afirka tana ƙara yawan kayan abincin da take saya daga ƙetare yayin da ƙasashe a nahiyar Asiya da kudancin Amirka suka samu gagarumin ci-gaba na albarkatun noma a cikin shekaru 20 da suka wuce.“

Katsalandan sojin ƙetare a Mali

Daga batun cimaka sai na rikicin tawaye. A shirye shiryenta na yin katsalanda a Mali, ƙungiyar tarayyar Turai EU za ta aike da jami'ai 200 da za su horas da sojojin ƙasar inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Militär Konferenz Mali
Hoto: Reuters

“Ko da yake halin da ake ciki a arewacin Mali inda ‘yan aware da kuma ‘yan ta'adda suka mamaye, mai matuƙar hatsari ne ga nahiyar Turai da kuma ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa, sai dai ba kamar yadda aka sa rai ba, tawagar sojojin da EU za ta tura Mali ba za ta yi girma ba. EU ta yanke shawarar aike wa da wannan adadi ne bisa darasin da ta koya a Somaliya inda a can ma tawagar da ta tura wadda ta horas da dakarun tsaron Somaliya ba ta wuci sojoji 200 ba. Sai dai bambamci da tawagar ta Somaliya wadda saboda rashin tsaro a cikin ƙasar, aka tsugunar da su a Uganda, horon da za a ba wa sojojin Mali a cikin ƙasar za a yi shi. Zai zama rashin basira a yi shi a wani wuri daban domin a Mali akwai dukkan tanade tanade da ake buƙata.”

Ƙarfafa rundunar Monusco a gabacin Kongo

Ita kuwa jaridar Financial Times a Jamus labari ta buga game da kiran da gwamnatin jamhuriyar demokraɗiyyar Kongo ta yi na a ƙarfafa rundunar Majalisar Dinkin Duniya a cikin ƙasar.

“Gwamnatin Kongo ta ba da fifiko da ɗaukar tsauraran matakan soji a yaƙin da ake yi da ‘yan tawayen da suka addabi gabacin ƙasar mai arzikin ƙarƙashin ƙasa. Jaridar ta rawaito Firaministan Kongo Augustin Matata na cewa ya zama wajibi a ƙarfafa tare da faɗaɗa aikin rundunar sojin Majalisar Dinkin Duniya wato Monusco, muddin ana son a tabbatar da tsaron kan iyakarta da Ruwanda, wadda ake zargi da tallafa wa ‘yan tawayen ƙungiyar M23 da ke aikata ta'asa a yankin arewacin Kivu. Duk wata tattaunawa ta siyasa da maƙwabciyar ƙasarsa ba ta tsinana komai ba, saboda haka dole a nemi wani zaɓi wanda ke da nufin ba wa rundunar Monusco damar kai farmaki cikin gaggawa.”

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe