Afrika cikin hotuna: Waiwayen abubuwan da suka faru a 2017
Fadi tashi a Afirka a 2017. A Zimbabuwe da Gambiya an kawar da shugabannin da suka dade a kan mulki, dambarwar zabe a Kenya da Laberiya. Yayin da hare-hare suka girgiza Somaliya da Najeriya.
Shugaban kama karya na Gambiya Jammeh ya rasa madafan iko
Jammeh ya yi mulkin kama karya a Gambiya tsawon shekaru 22. Ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa a watan Disambar 2016 wanda ya bashi mamaki. Sai bayan da kasashen Afirka ta Yamma suka tura sojojin ECOWAS ne sannan ya amince ya yi murabus a 2017. A watan Janairu 2017 Jammeh ya yi gudun hijira zuwa Equatorial Guinea bayan da ya kwashi dumbin dukiya daga asusun gwamnati.
Yuganda ta dakatar da neman madugun 'yan tawaye Kony
Joseph Kony, madugun kungiyar 'yan tawaye ta "Lord's Resistance Army" (LRA) kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya da ke The Hague tana nemansa ruwa a jallo. A watan Afrilu Yuganda da Amirka suka sanar da kawo karshen farautar Kony - a yanzu LRA ba ta da wani tasiri. Sai dai wasu rahotanni na Majalisar Dinkin Duniya sun ruwaito cewa LRA ta ci gaba da sace mutane a Kwango.
Fargabar fadawar Najeriya cikin rudani
Kasar wadda ke da mafi yawan jama'a a Afirka ta shiga rudani a 2017 na rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari mai shekaru 74 wanda ya shafe watanni uku a London bisa matsaloli na rashin lafiya, sannan kungiyar Boko Haram ta kai munanan hare-hare a Arewa maso Gabashin kasar. Miliyoyin mutane a yankin sun dogara ga taimakon abinci.
Dambarwar rikici a Kamaru
Mutane da dama sun mutu wasu sun jikkata bayan sanarwar ayyana 'yancin kan yankin Kamaru mai magana da harshen Ingilishi a watan Oktoba. Masu sa ido na kasa da kasa sun ce akalla mutane 40 sun mutu. 'Yan aware sun ayyana kafa jamhuriyar Ambazoniya. Yankin da ke amfani da harshen Ingilishi a Kamaru na ganin an mayar da su saniyar ware ana fifita masu amfani da harshen Faransanci.
Rudani bayan takaddamar zabe a Kenya
An rantsar da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a wa'adin mulki na biyu a matsayin shugaban kasa. An sake zabarsa a watan Agusta. Sai dai babban mai kalubalantarsa Raila Odinga ya ki amincewa da sakamakon zaben. Kotun koli ta soke zaben. Amma 'yan adawa sun kaurace wa zagaye na biyu na zaben. An yi zanga-zanga kuma mutane sun mutu.
Rikicin zabe a Laberiya
A watan Oktoba aka yi fatan zaben wanda zai gaji shugaba Ellen Johnson-Sirleaf. Bayan zaben wasu jam'iyyu biyu sun shigar da kara gaban hukumar zabe game da korafin da suke da shi. Sai dai kotun koli ta yi watsi da korafe-korafen, to amma a yanzu an sake gudanar da zabe tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai da tsohon gwarzon dan kwallon kafa George Weah, wanda ya yi nasara.
Yakin basasar Sudan ta Kudu ya haddasa yunwa
Shekaru hudu ke nan mutane a Sudan ta Kudu ke cikin wahala saboda rikici tsakanin magoya bayan Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar. Kashi daya cikin uku na al'ummar kasar sun tsere daga yankunansu na asali. Kimanin mutum miliyan biyar - wato rabin al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu na fama da yunwa. Rikici ya lalata kasa mai albarka inji Majalisar Dinkin duniya.
Mummunan hari a tarihin kasar Somaliya
Wata mota makare da nakiyoyi ta yi bindiga a wata hanya mai cike da zirga-zirgar jama’a a birnin Mogadishu a tsakiyar watan Oktoba, daruruwan mutane sun mutu. Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin wanda aka baiyana a matsayin mafi muni a tarihin kasar ta gabashin Afirka. Gwamnati ta zargi kungiyar al-Shabaab da kai harin.
Babu zaman lafiya a Mali
Shekaru shida kasar ta yammacin Afirka na fama da tashe-tashen hankula. Da farko juyin mulki, sannan boren ‘yan aware a arewaci daga nan rikicin ‘yan Jihadi. An sha kai hare-hare a kan sojoji dubu 11 na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin kiyaye zaman lafiya. A watan Janairu an kashe sojoji 77. Hari mafi muni kawo yau. Mayaka masu alaka da Alka’ida sun dauki alhakin harin na kunar bakin wake.
An kawar da Mugabe mai mulkin kama karya
Bayan shekaru 37 a karagar mulki, sojojin Zimbabuwe sun yi wa Mugabe daurin talala a gidansa bayan ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa domin dora matarsa. Mugabe mai shekaru 93 a wancan lokaci ya yi murabus yayin da ake shirin tsige shi. An rantsar da Mnangagwa shugaban kasa, sai dai ya ba da kunya ga wadanda suka tsammaci zai shigar da 'yan adawa cikin gwamnatinsa.
Kabila ya dage a karagar mulki
Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar demokradiyyar Kwango tuni ya yi wa’adin mulki sau biyu wanda kundin tsarin mulkin kasar ya amince da shi. Ko da yake wa’adinsa na biyu ya kare a 2016, ya ci gaba da daga zabe. A yanzu za a yi zaben a karshen 2018. 'Yan sanda sun dakile zanga-zanga a kan tituna, sun kuma kama masu zanga-zanga a cewar kungiyoyin adawa.
Badakalar cin hanci na kara fadi a Afirka ta Kudu
Zargin cin hanci a kan shugaba Afirka ta Kudu Jacob Zuma da attajiran iyalan Gupta sun yi kamari a cikin shekarar. An zargi kamfanonin waje da ba da toshiya domin samun kwangilolin gwamnati. Tattalin arzikin kasar ya yi rauni, rashin aiki ya kai kashi 30 cikin 100.