1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: 'Yan bindiga sun bude wuta kan masu zanga-zanga

Mohammad Nasiru Awal AH
October 29, 2019

A wani abin da ke zama daya daga cikin hare-hare mafi muni a kan masu zanga-zanga kyamar gwamnati, mutane 18 aka hallaka a birnin Karbala.

https://p.dw.com/p/3S8yd
Irak Proteste in Kerbala
Hoto: Getty Images/AFP

Jami'an tsaro a kasar Iraki sun ce a wannan Talatar wasu 'yan bindiga da suka rufe fuskokinsu sun bude wuta kan masu zanga-zanga a birnin Karbala mai tsarki ga 'yan Shi'a, inda suka hallaka mutane 18 sannan suka ji wa wasu daruruwa rauni.

Wannan na zama daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai kan masu zanga-zanga kyamar gwamnati da ta aka faro a farkon wannan wata.

Harin da aka kai a cikin dare ya zo ne lokacin da 'yan Iraki suka fantsama kan tituna kwanaki biyar a jere suna bore na zargin gwamnati da cin hanci da rashawa da rashin iya gudanar da harkokin mulki da dai sauran korafe-korafensu.

Ba a san wadanda ke da hannu a harin ba, masu zanga-zangar sun ce su ma ba su sani ba ko 'yan bindigar 'yan sandar kwantar da tarzoma ne ko dakaru na musamman ko kuma sojojin sa kai masu alaka da gwamnatin Iran. Suka ce an girke sojoji Iraki a kusa da wurin da suke zanga-zangar amma sun janye lokacin da maharan suka fara harbi da gas mai sa hawaye da kuma bindiga.