1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akalla mutane shida sun rasu a wani hari a Turkiyya

Mohammad Nasiru AwalAugust 15, 2016

Fashewar wani abu ya hallaka mutane a wani caj ofis da ke yankin Kurdawa da ke kudu maso gabashin kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/1Jiiz
Türkei Region Diyarbakir Bombenanschlag
Hoto: Reuters/Ihlas

A wannan Litinin 'yan tawayen Kurdawa sun tada wani bam a wani caj ofis da ke kudu maso gabashin Turkiyya inda suka hallaka 'yan sanda hudu da farar hula biyu, tare da yi wa akalla 21 rauni. Mukaddashin Firaministan Turkiyya Numan Kurtulmus ya fada wa manema labarai cewa wani yaro na daga cikin wadanda suka rasu a harin da ya auku a birnin Diyarbakir.

Ya ce: "Jami'an 'yan sanda hudu da fararen hula biyu ciki har da wani karamin yaro dan wani dan sanda aka kashe a harin. A jimilce mutane shida suka yi mutuwar shahada."

Mahukunta sun zargi kungiyar Kurdawa ta PKK da hannu a harin. Akalla mutane 12 aka hallaka a wani jerin hare-hare da PKK ta kai kan 'yan sanda da sojojin Turkiyya a yankin Kurdawa da ke kudu maso gabashin kasar a makon da ya gabata.