1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko an dau darasi a zanga-zanga?

August 9, 2024

A yayin da ake shirin kare kwanaki 10 na zanga-zangar neman sauyi a Najeriya, daga dukkan alamu masu mulkin kasar sun dau darasi kan dangatakar da ke tsakaninsu da talakawa.

https://p.dw.com/p/4jJ4S
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Zanga-Zanga | Tasiri | Tsadar Rayuwa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sodiq Adelakun/AFP

Duk da cewar dai zanga-zangar ta rikide daga gwagwarmaya ta neman sauyi ya zuwa wasoso na da dama a wasu jihohin kasar, yanayin na shirin bude sabon babi cikin kasar a halin yanzu. An dai dauki lokaci ana kallon-kallo, a tsakanin talakawan da ke fadin ana musu mulki maras kyau da kuma su kansu masu mulkin da ke fadin talakawan ba su da imani balle su sadaukar da rayuwa domin ginin kasa. Kafin zanga-zangar da ta hade kan arewacin kasar da kudancinta, kuma ta aika babban sako cikin kasar a halin yanzu. Neman korar yunwar dai ya hade kan talakawan da suka yi watsi da kirayen sarakuna da malamai, ko bayan kokarin rabon kudi da niyyar raba kai. A Abuja dai alal ga misali sama da Naira miliyan dubu 22 ne majiyoyi suka ce an badda, a kokarin kau da hankalin matasan ba kuma tare da kai wa ya zuwa hana hawa na tituna cikin neman sauyin ba. 

Najeriya | Zanga-Zanga | Tasiri | Tsadar Rayuwa
Daga tutocin Rasha yayin zanga-zanga a Najeriya, na janyo tambayoyiHoto: Christine Mhundwa/DW

A wani abun da ke nuna alamun karshen tasiri na kudi da kila ma bambancin addini da kabila, cikin batutuwan Tarayyar Najeriyar. To sai dai kuma zanga-zangar ta tono rikici na talaucin da ke cikin arewacin kasar, inda matasan suka rika wasoso har na abubuwan da ba su da tasiri ga tattalin arziki. Zanga-zangar dai, ta tabbatar da hasashen yankin na zama na kan gaba cikin batun na talauci a duniya baki daya da kuma barazanar da talaucin ke iya yi ga makoma ta daukacin kasar. Tuni dai Abujar ta fara nuna alamun koyon darasi, tare da jeri na matakan damar ilimi da kila kokarin rage radadin na talauci. Kuma ko bayan nan dai, masu mulkin sun kuma nada wasu jami'ai guda shida da suka dorawa alhakin sauraron al'umma a shiyoyi guda shidan da ke Najeriya a halin yanzu. A bun jira a gani dai na zaman tasirin zanga-zangar a cikin lamuran mulki da siyasa cikin kasar da ke nuna alamu na tsunduma a siyasar gobe, tun daga safiya ta wannan mako.