al-Assad na da tabbacin lashe zaben Siriya
June 3, 2014Al'ummar Syriya sun fara kada kuri'a da nufin zaben shugaba kasa, a daidai lokacin da ake ci gaba da ba wa hamata iska tsakanin dakarun Bashar al-Assad da kuma masu neman ganin bayan mulkinsa. Mutane uku ne suka tsaya takara, wato shugaba mai ci Bashar al-Assad da kuma masu kalubalantarsa su biyu da ba a san su ba. Mutane miliyan 15 ne dai suka cancanci kada kuri'a a zaben da ake hasashen cewa shugaba mai ci yanzu wato Bashar al-Assad zai lasheshi.
'Yan Syriya da dama ne dai ba za su samu damar yin zabe ba saboda kashi 40 daga cikin 100 na al'ummar kasar sun kaurace wa matsugansu sakamakon yakin da ya daidaita kasar. Zaben dai zai gudana ne a yankunan da ke karkashin ikon gwamnati ne kawai.
Kasashen yammacin duniya sun yi kira ga shugaba Assad da ya sauka daga kujerar mulki, domin kawo karshen yakin da aka fara a shekara ta 2011, wanda kuma ya lamshe rayukan kimanin mutane dubu 160.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu