1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Burhan na son hawa teburin tataunawa da RSF

Binta Aliyu Zurmi
September 23, 2023

Jagoran gwamnatin mulkin soja a Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce a shirye ya ke ya hau teburin tataunawa bisa wasu sharudda nasa domin kawo karshen rikicin da suke yi da dakarun RSF.

https://p.dw.com/p/4Wimo
UN-Generalversammlung | Abdel-Fattah Al-Burhan Abdelrahman Al-Burhan
Hoto: Craig Ruttle/AP/picture alliance

A jawabinsa a gefen zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York janar al-Burhan ya ce ko wane yaki na karewa ne a hanyoyi biyu imma dai ta ala dole wani bangare ya saduda ya mika kai ko kuma ta hanyar hawa teburin sulhu. Ya kuma ce hanyar da suka zaba ita ce ta sulhu.

Jagoran sojin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, kazalika ya kuma umurci kasashe makwabtan Sudan da su daina taimakawa rundunar sa kai ta RSF da makamai.

Ya kara da cewar yana mai kyakyawan zato shiga tsakani da kasashen Saudiyya da Amurka ke yi ka iya kawo karshen rikicin da suka kwashe watanni biyar suna yin shi kwata-kwata.

Tun a tsakiyar watan Fabarairu ne kasar ta Sudan ta fada cikin rikicin shugabanci, wanda har kawo yanzu ake ci gaba da lugudan wuta musamman ma a yankunan Khartoum da Dafur da tuni ya rikide ya zuwa na kabilanci.

Al-Burhan ya ce babban buurinsa a yanzu haka shi ne lalubo hanyar kawo karshen wannan rikicin da ya kashe dubban al'umma da kiuma raba miliyoyi da matsugunnansu.