1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta dauki alhakin hari kan wata jami'a a Kenya

Mohammad Nasiru AwalApril 2, 2015

Sai dai har yanzu kungiyar ta masu kaifin kishin addini daga Somaliya, ba ta fito a hukumance ta ce ita ta kai harin ba.

https://p.dw.com/p/1F25J
Kenia Attentat in Garissa
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wani babban kwamandan al-Shabaab ya ce kungiyar ta masu kaifin kishin addinin ta Somaliya ke da hannu a harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata jami'a ta gabashin kasar Kenya inda suka hallaka akalla mutane 15 suna suka yi garkuwa da wasu. Sai dai har yanzu kungiyar ba ta fito a hukumance ta dauki alhakin harin da aka kai kan jami'ar Moi da ke garin Garissa mai tazarar kilomita 350 gabas da birnin Nairobi. Wani dalibi a jami'ar ya yi karin haske dea cewa suna barci suka ji karar harbe-harbe da misalin karfe biyar na asuba. Sun tashi suna neman wurin gudu. Amma abin bakin ciki sai wasunsu suka fuskanci wurin da harbin ke fitowa. Amma daga bisani sun samu sa'ar fita daga harabar makarantar.

Ministan cikin gidan Kenya Joseph Nkaissery ya tabbatar da mutuwar mutane 15 sannan fiye da 60 sun jikkata.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya mika ta'aziyarsa ga 'yan uwan wadanda ta'asar ta rutsa da su.