al Shabaab ta kakkabo jirgin yakin Kenya
December 4, 2014Wani jirgin yakin kasar Kenya ya fadi a kudancin birnin Kismayu na Somaliya, bayan wani aikin shawagi da ya gudanar a yankin da kungiyar al-Shabaab ta saba tayar da kayar baya a cikinsa. Tuni ma dai wannan kungiya dake da kaifin kishin addini ta daukin alhakin wannan hari. Kakakin kungiyar Abdiasis Abu Musab ya ce sun yi amfani ne da makami mai linzami a wajen kakkabo wannan jirgi a garin Baluguduud. Da ma dai sojojin kasar ta Kenya suna cikin runkunin dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Affirka da aka jibge a KIsmayo bayan da aka kwato garin daga hannu masu kaifi kishin addini.
Jaridun kasar ta kenya ta suka ruwaito wannan labarin suka ce ba su da masaniya game da yawan mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikata. Sai dai kuma hadarin jirgin ya zo ne makwani biyu bayan da kungiyar al-Shabba ta kai tagwayen hare-hare a arewacin Kenya wadanda suka lamashe rayukan mutane sama da 60.