Al-Shabab ta ce babu 'yunwa a Somaliya
July 22, 2011Ƙungiyar Al-Shabab ta Somaiya da ke da tsananin kishin addinin musulunci ta sa ƙafa ta yi fatali da rahoton da Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta fitar da ke nuna cewar 'yunwa ta afkawa ƙasar. Kakakin ƙungiyar Sheikh Ali Mohammad Rage ya bayyana cikin wata hira da yayi da gidan radiyon Al-Furqaan a yau Jumma'a cewar labarin 'yunwa shafcin gizo ne, kana siyasa ce tsagwaranta. Ko da shi ke dai kakakin na Al shabab ya amince cewar wasu yankunan ƙasar ta Somaliya sun gamu da kanfar ruwa, amma kuma ya ce haramcin da ƙungiyar ta sanya wa wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na nan daram daƙam.
Wannan sanarwar ta Al-shabab, ta zo ne 'yan makwanni bayan amincewa da ta yi cewar asusun tallafawa ƙananan yara ta MDD wato UNICEF ya kai agajin abinci da magunguna a yankunan da ke ƙarƙashin ikonta. Masu sanya idanu akan abubuwa da ke wakana a ƙasar ta Somalia na ganin cewar wannan sabon matsayin da ƙungiyar ta ɗauka zai sake taɓarɓara matsalar 'yunwa da ake fama da ita a ƙasashe somaliya, da Habasha da kuma wani ɓangare na kenya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu