Al'adun kabilar Turkana da ke kasar Kenya.
Misali karuwar gina madatsun ruwa da tonon rijiyoyin mai, na daga cikin abinda ke barazana ga makomar kabilar, amma dai suna ci gaba da yawo da garakensu yankin yammacin kasar Kenya.
Kare kadarorinsu
Kabilar Turkana suna rayuwa ne a yankin Arewa maso Yammacin kasar Kenya, a kusuruwar Illemi da ake takaddama kanta, sanadiyyar ikirarin mallakar ta da kasashen Habasha da Sudan ta Kudu suma ke ikirari. Domin kare kansu da dabbobinsu daga mahara, Turkanawa na sabar bindiga tun suna matasa. Samari na kiwon dabbobi tun a kuruciyarsu.
Rayuwar makiyaya
Turkanawa sukan kwashe daukacin shekara suna yawon neman wuraren kiwo da mashaya wa dabbobinsu a cikin dazuka da ke fama da fari. Suna kiwon rakuma, shanu, jakuna da awaki. Musamman matansu na fiskantar tsananin rayuwa. Suna daukar kaya mai nauyin gaske a kawunansu, kana hakkinsu ne ciyar da iyalai da sauran ayyukan cikin gida.
Dutsen yuwa a matsayin alama
Matan Turkana suna yin ado da sarkar gargajiya wando su ke sakawa da kansu. Sarkar na zama alamar matsayin mace. Matar da bata da irin wannan adon yuwa, ta kan sha wahalar samun na miji da zai aure ta. Yawan sarkar yuwa da mace ta saka na zaman babban hanyar da za ta samu wanda ta ke so. Akasarin mazajen kabilar na auren fiye da mace daya.
Cikin ado a ko wane lokaci
Turkanawa na yin adonsu ne da gilasai, ‘ya’yan itace, wuri, kokon dabbobi irinsu dodon kwadi da makamantansu, karafuna ko gwangwanaye. Suna cire adonsu ne kawai in wata cuta ta kama su, ko suna zaman makokin mutuwar dan uwansu. Komai tsufar Turkunawa suna yin ado.
Cikin tafiya ko da yaushe
Matar Turkana dauke da kayanta bisa hanyar kaura. Iyalan na hanyarsu tayin kaura a sabon wurin da ke da yabanyar kiwo. Cikin garaje yarta na barci kan jaki. Yawan Turkanawa bai kai miliyan guda ba, wato sune kashi biyu da rabi na al’ummar Kenya.
Wanka a rafi
Bayan doguwar tafiya, matan da yaran na yin wanka. Za su yi wanki kana su debi ruwan sha. Turkanawa na daukar karnuka a matsayin dan uwa cikin danginsu. Suna amfani da kashin karnuka a matsayin magani. Misali sukan shafa a wuyarsu don maganin kuraje kafinsu dora dutsen wuya mai nauyi.
Kayan ado mai kaifi
Wani mutumin Turkana sanye da wuka da aka yi ta matsayin adon hanu. Ana amfani da ita wajen kare kai, ko kuma yankan nama. Turkanawa sun dogara da dabbobinsu a matsayin abin ci, wato nama da madara dama jinin dabbobin.
Sabon abin ci
An samu sauyi matuka a rayuwar Turkanawa, amma ga aksarinsu har yanzu cin kifi na mastayan haramun. Amma koda yake Turkanawan a yanzu suna karya wannan al’adar suna cin kifi, kamar tarwadan da ake samu a tabkin Turkana.
Busashen kifi
A wuraren da ke fama da fari, ana stumin busashen kifi a matsayin abinci mai gina jiki. Ana kamo kifin a fadamun kusa da tabkin Turkana, kana a shanya su kan igiya inda ranan ke busar da su. A kabilar Turkana kamun kifi aikin maza ne.
Gadi cikin dare
Kai hare-hare da makamai kana da satar shanu, sun zama ruwan dare a yankin Turkana da ke fama da tashe-tashen hankula. Haka kuma rike makamai kamar su mashi, kwari da baka, kana a yanzu Turkanawa na yawan yin amfani da bindigogi. Suna sintiri har fitowar rana.