1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden na ziyara a Gabas ta Tsakiya

Mahamud Yaya Azare LMJ
July 13, 2022

Shugaban Amirka Joe Biden na ziyara irinta ta farko a Gabas ta Tsakiya, wacca ya farota daga Isra'ila kafin ya zarce zuwa yankunan Falasdinawa da kuma kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4E5UH
Isra'ila | Ziyara | Joe Biden
Shugaban Amirka Joe Biden ya samu kyakkyawar tarba a AmirkaHoto: MENAHEM KAHANA/AFP

Ziyarar da tun kafin farata aka bayyana cewa babban jigonta shi ne inganta tsaron Isra'ila da kawayen Amirka da ke yankin, tare da yunkurin zawarcin karin kasashen yankin domin su kulla hulda da Isra'ila da kara mayar da Iran saniyar ware. Daga bisani kuma za a yi batun farfado da shirin zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra'ila. Gwamnatin rikon kwaryar Isra'ila dai ta zuba ruwa a kasa ta sha domin murnar wannan ziyarar da take ganin za ta ba ta damar cimma nasarorin da za ta iya yin gangamin yakin neman zabe da su.

Yarjejeniyar Qudus da aka shirya za a rattaba hannu a kanta tsakanin firaministan Isra'ila da shugaban Amirka yayin ziyarar dai, za ta kara bai wa Isra'ilan lamunin tsaro daga duk wata barazanar ketare ko  hare-haren makiya da kuma ake sa ran fadadata ta hade da tsaron kawayen Amirka a yankin. Duk da jaddada goyan bayansa ga kafuwar kasar Falasdinu da Biden ya yi, hukuma Falasdinawan ta bakin kakainta na ganin hakan tamkar raina musu hankali ne kawai.