Alamun cutar Ebola
January 14, 2015Talla
Alamun kamuwa da cutar Ebola kan bayyana ne tsakanin kawanaki 2 zuwa 21 bayan shigar cutar jikin bil Adama. A wasu lokuta alamun kan bayyana tsakanin kwanaki 8 zuwa 10 bayan an kamu kuma suna kama ne da alamun kamuwa da zazzabin cizon sauro (malaria) ko mura. Alamun dai sun hada da:
Zazzabi
Kumallo
Gudawa
Ciwon makogaro
Ciwon kai
Ciwon jiki
Ciwon ciki
Kasala
Rashin son cin abinci
Ba lallai ne dukkan wadannan alamun su bayyana ba, wasu suna iya ganin alamu biyu kacal, misali jini na iya fitowa daga kafofin wadansu daga yikin bangarorin jikin mutun, wadanda suka hada da hanci, da baki da kuma al'aura