1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alhinin mutuwar Morgan Tsvangirai

Abdullahi Tanko Bala
February 15, 2018

A Zimbabuwe da ke makwabtaka da Afirka ta Kudu Allah ya yi wa madungun adawa na kasar Morgan Tsvangirai rasuwa bayan fama da cutar daji wato cancer.

https://p.dw.com/p/2sjzl
Simbabwe - Morgan Tsvangirai
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Auntony

An haifi Morgan Tsvangirai a shekarar 1952. Mahaifinsa manomi ne kuma ma'aikacin hakar ma'adinai. Tsvangirai ya bar makaranta da kuruciya, ya yi aiki na tsawon shekaru goma a mahakar ma'adinai inda ya zama daya daga cikin shugabannin kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai. A matsayin dan kwadago ya shiga jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a 1980 a farkon lokacin mulkin kai. Kamar wasu 'yan kasar da dama a wancan lokaci, yana kaunar Mugabe an kuma soke shi daga baya saboda kin yin Allah wadai da dirar mikiyar da aka yi wa 'yan adawar Zimbabuwe a Matabeleland a karshen shekarun 1980.

Ba abu ne mai sauki ba ja da mutum kamar Robert Mugabe a fagen da ya yi shura a kansa. Samun karbuwa da shiga zuciyar 'yan Zimbabuwe ko shakka babu fage ne da Mugabe ya taka rawar gani tsawon shekaru da dama. To amma Morgan Tsvangirai ya yi kokarin kada shi a lokuta da dama.

Zimbabwe Oppositionsführer Morgan Tsvangirai
Tsvangirai dan fafutika da ya nemi kawo sauyiHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Ga misali zaben 2008 wanda Tsvangirai ya lashe ko da yake da dan kankanin rinjaye. Sannan da garanbawul wanda da ya sami wuce wa da ya bai wa Mugabe karin karfin iko, amma Tsvangirai da sauran shugabannin adawa suka yi nasarar dakatar da wannan. Tsvangirai ba da shi a ka yi gwagwarmayar kwatar 'yanci ba domin Mugabe ya girme shi da ratar kusan shekaru 30 amma ya yi kokarin zama jigon 'yan adawa a Zimbabuwe kuma babban mai kalubalantar Mugabe.

Ostalos Gift Sisiba shugaban kungiyar dalibai ta Zimbabuwe ya yi tsokaci da cewa: "Da ba dan Morgan ba da ba za mu yi magana a kan dimokradiyya ba, ya yi gwagwarmaya da 'yan mulkin kama karya tun a 1990 lokacin da Robert Mugabe ke mulkin mulaka'u"

A tsakiyar shekarun 1990 ne Tsvangirai ya fito fili ya fara sukar gwamnatin Mugabe. Tsvangirai ya jagoranci gagarumar zanga-zanga da yajin aikin ma'aikata. Ya yi fafutukar kwato 'yancin ma'aikata a Zimbabuwe a cewar Morgan Komichi mataimakin shugaban jam'iyyar MDC ta Tsvangirai. A lokacin Tsvangirai yana dan jam'iyyar ZANU-PF, a yayin da yake sakataren majalisar kungiyoyin kwadago, tare da hadin gwiwar dalibai da kungiyoyin coci ya zama shugaban majalisar kasa ta kungiya mai zaman kanta wadda ta rika shirya zanga zanga da kuma sukar lamirin gwamnatin ZANU-PF.  A 1999 Tsvangirai ya kafa kungiyar gwagwarmayar dimokradiyya MDC wadda ta rikide ta zama babbar jam'iyyar adawa.

Robert Mugabe und Grace Mugabe
Mugabe me mafarkin dawwama a mulkiHoto: Getty Images/J.Njikizana

Robert Mugabe ya so ya dawwamar da tsarin jam'iyya daya a kasarsa shawarar da 'yan Zimbabuwe suka aminta da ita a cewar Siziba na kungiyar dalibai ta kasa. Ya ce da Morgan Tsvangirai ya kawo sauyi a lamuran siyasa da dimokradiyya ba abu ne mai sauki ba. A shekarar 2002 Tsvangirai ya yi yunkurin farko na zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar MDC.  A shekarun 2000 an sha shige da fice a gidan yari inda ake kulle shi sannan a sako shi bisa zargin cin amanar kasa ko shirya yunkurin kashe Shugaba Mugabe. An ci zarafinsa sosai a hannun 'yan sanda wanda har sai da aka kwantar da shi a asibiti sakamakon tsagewar kokon kansa.

A 2008 lokacin da duniya ta juya wa Zimbabuwe baya, an dauki Tsvangirai a matsayin mutumin da ya fi dacewa wajen magance matsalolin siyasa da na tattalin arziki da suka yi wa kasar katutu. A yunkurinsa na biyu na neman shugabancin kasar, ya ci zabe a hakika to amma bai sami rinjayen da ake bukata ba domin kafa gwamnati. Shugaba Mugabe ya lashe zaben da aka sake gudanarwa bayan da Tsvangirai da 'yan adawa suka kaurace wa zaben bisa hujjar cewa ba za'a yi adalci ba. Abin da ya biyo bayan nan shi ne shawarwarin kafa gwamnati da a ka yi ta yi tsawon watanni kan rabon madafun iko wanda Afirka ta Kudu ta shiga tsakani. Tsvangirai dai bai sami nasarar kada Mugabe ba amma ya sami damar shiga gwamnati a matsayin firaminista inda aka yi rabon iko tsakanin ZANU-PF da 'yan adawa. 

Simbabwe: Robert Mugabe und Morgan Tsvangirai Flash-Galerie
Mugabe da Tsvangirai Hoto: picture alliance/dpa

Gwamnatin hadakar dai ta kasance ne na zangon mulki daya kacal, to amma Tsvangirai na jin cewa Mugabe da jam'iyyarsa ta ZANU-PF ke juya akalar lamura. Ya bata lokaci yana zagaye kasashen duniya a wani yunkuri na kyautata dangantaka da gwamnatoci na kasashen waje da cibiyoyi na kasa da kasa. A wata hira da DW Tsvangirai ya amince cewa 'yan adawa sun sami rauni sosai:"A lokacin da MDC ta shiga hadakar gwamnati da ZANU-PF mun yi ne domin bauta wa al'umma ba don wani abu ba, mun yi kawancen ba yadda aka so ba to amma ina jin mun yi kokarin ceto kasar".

A karshen 2017 Tsvangirai ya yi maganar cewa lokaci ya yi da sabbin jini za su karbi ragamar mulki a Zimbabuwe, yana mai cewa ina ganin ya kamata mu tsofaffi mu ja baya mu sanya matasa a gaba su ci gaba da ayyukan da muka faro. Mugabe mai shekaru 93 a lokacin da aka atilasta masa yin murabus da ni mai shekara 65 mun zama 'yan mazan jiya. Abin tambaya da kuma lura na zama yaya al'umma ta gaba za ta cigaba wannan ya kamata mu yi la'akari da shi. A cewar Tsvangirai.