Ali Khamenei ya bude kofar tattaunawa da Amurka kan nukiliya
August 27, 2024Jagoran addini na kasar Iran Ayatollah AliKhamenei ya fada wa al'ummar Iran cewa babu wani shinge da zai hana tattaunawa da makiyi. Kalaman nasa na nuna yiwuwar zantawa a karkashin mulkin sabon shugaban kasar mai ra'ayin sauyi Masoud Pezeshkian sannan ya kara sabunta gargadinsa na cewa Amurka ba kasar da za a yarda da ita ba ce.
Khamenei ya nemi fitowar masu zabe
Sai dai, ana ganin kalaman na shugaban addinin na kama da irin wadanda ya yi a 2015 a lokacin da kasar ta rage aikin makamin nukiliyarta bayan zantawa da manyan kasashen duniya inda aka sassauta mata wasu daga cikin takunkuman tattalin arziki. Ya kara da cewa kasar ba za ta dora fatanta a kan makiya ba, sannan ba za ta jira makiya su amince da tsare-tsarenta ba.
Iran ta kore shakku kan kashe Shugaba Raisi aka yi
A wasu lokuta Khamenei mai shekara 85 ya nemi tattaunawa da Amurka sannan a wasu kuma ya shiriritar da batun musamman a lokacin da tsohon shugaban kasar Amurkan Donald Trump ke shugabanci.