Alkalan kotun koli byu sun mutu a Afghanistan
January 17, 2021Talla
Da sanyin safiyar yau ne maharan dauke manyan bindigogi, suka saita matan alkalan kotun kolin kasar, kuma suka bindige su a harin tare da jikkata drebansu, a cewar kakakin kotun kolin Ahmad Fahim Qaweem.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da babban birnin Khabul na Afghanistan ke fama da jerin hare-haren ta'addancin da ake zargin kungiyar Taliban ce ke kai su.
Bisa shiga tsakanin Amirka, har yanzu ana samun jan kafa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan Taliban don tabbatar da zaman lafiya a kasar, yarjejeniyar da ta ba wa Amirkar damar soma janye dakarunta da ke kasar.