Alkawarin hana yaduwar makaman nukiliya
January 3, 2022Talla
A sanarwar bai daya da suka fitar kasashen wadanda suka hada da Amirka da Rasha da China da Birtaniya da kuma Faransa sun jaddada cewa yaki da makamin nukiliya ba zai haifar da nasara ba a saboda haka bai kamata a fara amfani da shi ba kuma ya zama wajibi a hana yaduwar makaman na nukiliya.
Kasashen wadanda dukkanin su suke da ikon hawa kujerar na ki sun fidda sanarwar ce kwana guda gabanin taron da za a gudanar kan hana yaduwar makaman nukiliya, dokar da aka dabbaka a shekarar 1970.
Sanarwar dai na zuwa ne yayin da aka koma tattaunawa a birnin Vienna domin farfado da yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran wadda ke kokarin mallakar makamin na kare dangi.