Bukatar agajin gaggawa a Ethiopiya
November 16, 2022A karshen makon da ya gabata ne gwamnatin Ethiopia da 'yan tawayen kungiyar TPLF masu fafutuukar neman 'yancin Tigray suka cimma yarjejeniyar bada damar kai agaji ga duk bangarorin da ke bukata a cikin gagawa, a wani zama da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya.
Dukkanin bangarorin sun rattaba hannu a kan samar da isashen tsaro ga ma'ikatan jinkai a yankunan Tigrai da kewaye.
Yanzu haka kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin agaji na jiran amincewa jami'an tsaro domin isar da kayayakin agaji ga mabukata musamman a yankunan yankin Tigray da yaki ya daidaita. A jawabinsa ga 'yan majalisar wakilan kasar firaminista Abiy Ahmed ya ce yaki ba shi da dadi ko da kuwa ga bangaren da ya yi nasara ne.
Ya ce "Yaki sunan shi ma ba shi da dadi samsam, balle a kwatanta shi da kalaman nan da ake cewar nasara a yaki, yaki ko bangaren da ya yi nasara ne bai da dadi, don ko ta yaya an salwantar da rayukan mutane da kuma kashe makudan kudi. babu wata nasara a tattare da yaki. Yanzu haka dai mun cimma yarjejniyar dawamammen zaman lafiya mun rattaba hannu kuma dole ne mu cika alkawarin da muka dauka na samar da zaman lafiya".
Kafin cimma wannan matsaya ta samar da hanyar da za a isar da kayayyakin agaji ga al'ummar yankin Tigray, gwamnatin firaminista Abiy Ahmed ta ce ta jima da fara samar da gudumawar gwamnati ga wannan yankin, sai dai a cewar hukumar lafiya ta WHO mafi akasarin cibiyoyin lafiya a yankin a rufe suke yayin da wadanda ke bude kuma babu komai a cikinsu saboda rashin kayayyakin aiki.
Shugaban hukumar ta Lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda a baya ya ziyarci yankin na tigray ya jaddada mauhimmancin samar da magunguna gami da abinci. Dr Michael Ryan shi ne babban darakata a hukumar WHO:
Ya ce "al'ummar yankin Tigray na masu bukatar kayayyakin abinci da magunguna masu tarin yawa, ba wai tsugul-tsugul ba, saboda sun shafe sama da watanni 16 ba su sami wani agaji ba wanda hakan ya sanya su a cikin wani hali na tagayyara".
Wannan yanki na Tigray dai ko baya ga yarjejeniyar tsagaita wuta ta watanni biyar da aka samar a baya, ba su sami agajin da suke bukata ba, lamarin da ya ta'azzara rashin abinci da magunguna ga sama da mutum dubu 40 da ke dauke da cutar HIV da ma wasu masu fama da tarin fuka.
A farkon wannan watan ne gwamnatin Ethiopia da kungiyar TPLF suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin, wanda ake cike da fatan ganin dorewarta.