Yan gudun hijira sun jefa jama'a cikin yanayin fargaba
March 8, 2019Talla
Zargin fyade da sace-sace na daga cikin dalilan da suka saka hukumomi kebe 'yan gudun hijirar, amma bayan kwashe lokaci suna rayuwa a sansanin aka soma samun labarin yunkurin tayar da rikici da sunan jan hankulan hukumomin Nijar don basu takardar shedar zaman, amma a cewar Gwamnan na Agadez, Sadou Soloke, da ya ziyarci sansanin, ya ce ba za su amince da duk wani yunkuri na tada zaune tsaye ba, ya kara da cewa, babu wani dalili na matsawa gwamnati kafin ta bayar da takarda, ya shawarci 'yan gudun hijirar da su kwantar da hankulansu har sai an kamalla bincike.