Al'ummar duniya na yin bukukuwan Kirismati
December 25, 2016Daga nasa bangare a hudubar da ya gabatar a daran jiya Asabar a fadarsa ta Vatican a gaban mutane dubu 10, Paparoma Francis jagoran Kiristoci mabiya darikar katholika a duniya ya yi kira ga a tausaya wa kananan yara musamman wadanda yake-yake dama talauci ya saka a cikin halin kunci inda ya yi karin bayani yana mai cewa:
" Muna da babban kalubale a gabanmu na kananan yara, ka dauka tun daga wadanda aka tauye wa 'yancin zuwa duniya da wadanda ke kuka sabili da yunwa da wadanda suka rasa kayan wasa a hannunsu sai dai makamai."
Sai dai a kasashen Turai da dama ana ci gaba da gudanar da shagulgullan bikin Kiristimetin na bana a cikin tsaurararn matakan tsaro sabili da fargabar da ake da ita ta yiwuwar fuskantar hare-haren ta'addanci kasancewa bikin ya zo ne kwanaki kalilan bayan harin da aka kai a kasuwar Kiristimatin birnin Berlin na kasar Jamus da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.